Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bamabamai Sun Sake Tashi cikin Maiduguri


Jami'an tsaro na kwashe wadanda suka jikata
Jami'an tsaro na kwashe wadanda suka jikata

A daidai lokacin da sojoji ke ikirarin samun galaba kan 'yan kungiyar Boko Haram a yakin da su keyi sai gashi 'yan ta'adan na kara yawan tada bamabamai cikin Maiduguri da kewaye

Da misalin karfe bakwai da rabi na daren jiya Lahadi aka sake samun tashin tagwayen bamabamai cikin birnin Maiduguri fadar gwamnatin jihar Borno.

Bamabaman sun hallaka mutane tare da raunata wasu da dama. Bamabaman sun tashi ne a wurare hudu daidai lokacin da ake gudanar da sallar isha.

Bamabamai biyun da ya tashi a wani masallaci ya hallaka wasu da dama.

Hakazalika bam na uku ya tashi ne a wani wuri da ake cajin waya da inda yara ke wasan bidiyo.

Bam na hudu ya tashi ne a anguwar atilari inda mata ke toye-toye irin na dare.

Kawo yanzu ba'a iya tantace adadin wadanda suka rasa rayukansu ba tare da wadanda suka jikata.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:04 0:00
Shiga Kai Tsaye

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG