Mayakan Boko Haram dake gujewa daka hare-haren da dakarun sojojin Najeriya ke kai masu a sansaninsu dake dajin Sambisa suna farke fushinsu kan kauyukan da basu da jami'an tsaro.
A karshen mako sun sake kai hare haren sari ka noke a wasu kauyukan karamar hukumar Madagali dake kan iyakan jihohin Adamawa da Borno.
Mayakan sun kai hari a kauyukan Sabongari da Dutse Biyu kuma kawo yaznzu ba'a tantance adadin wadanda aka kashe ba. Maharan suna fakewa ne cikin duwatsu da dazukan dake kewaye da yankin.
Sakamakon karancin jami'an tsaro a yankunan da sojoji suka kwato 'yan banga ne suke taka muhimmiyar rawa wajen kare yankunan.
Al'ummar yankin na rokon gwamnati da ta kai masu doki cikin gaggawa. Wani ganao yace bayan maharan sun bar Sabongari sun farma Kafin Hausa inda suka yi kashe kashe tare da kone gidaje.
Kazalika dan majalisa dake wakiltar yankin ya sake tabbatar da kashe mutane ba iyaka tare da kone gidaje. Saboda haka ya kira gwamnati ta jibge sojoji a yankin.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.