Dan majalisa dake wakiltar yankunan Michika da Madagali dake arewacin jihar Adamawa a majalisar wakilan Najeriya, Adamu Kamale ya byyana halin da mutanensa ke ciki.
Damuwar itace babu abinci a kauyuka da garuruwan idan kuma an kawo abinci sai gwamnati ta ajiye a wasu sansanonin 'yan gudun hijira inda yanzu babu mutane da yawa kamar kauyukan da mutane suka koma. Maimakon a ajiye abinci a cikin gari kamata ya yi a kai kauyuka a rarrabawa mutane.
A wani yunkurin taimakawa al'umma kungiyar kasa da kasa ta Red Cross ko ICRC a takaice ta kaddamar da gidauniyar kayan abinci da na harkokin yau da kullum. A jihar Adamawa 'yan gudun hijira kusan 7,000 suka samu tallafi daga gidauniyar.
Malam Aliyu Maikano jami'in kungiyar Red Cross a shiyar arewa maso gabas ya bayyana dalilan bada tallafin.
Kungiyar na bada tallafi ne akan fannin da ya shafi lafiyar mata da yara tare da bada kayan abinci da basu kayan kwanciya da kiran wasu kungiyoyin su bi sahunsu
Gwamnan jihar Adamawa ya musanta zargin rashin kula da 'yan gudun hijiran da ma wadanda suka koma kauyukansu. Yace hukumar bada agajin gaggawa ta jihar tana iyakacin kokarinta da raba kaya.
Ga karin bayani.