Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Rigima ta Kunno Kai Tsakanin Gwamnatin Borno da Wasu 'Yan Gudun Hijira


Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima
Gwamnan jihar Borno Ibrahim Shettima

Wata rigima ta kunno kai tsakanin wasu 'yan gudun hijira daka garin Baga dake karamar hukumar Kukawa da gwamnatin jihar Borno

Rigimar ta samo asali ne domin gwamnatin jihar tace ita bata san da zamansu ba.

Kwanaki biyu da suka gabata 'yan gudun hijiran suka shiga garin Maiduguri daga Baga sakamakon yunwa da suka ce suna fama da ita a garin tun lokacin da suka koma. Mutanen sun koma Bagan ne lokacin da rundunar sojin Najeriya ta sake kwato garin daga hannun 'yan Boko Haram amma ba da sanin gwamnati ba.

'Yan gudun hijiran sun zargi gwamnati da cewa tun lokacin da suka koma Baga gwamnati bata ziyarcesu ba ko ta aika wani ya ga halin da suke ciki. Bugu da kari sun yi zargin cewa sojojin dake garin suna hana shiga ko fitar da abinci. Ban da haka wai sojojin sun hanasu yin sana'arsu ta kamun kifi ko yin noma. Sun ce lamarin ya jefasu cikin halin kakanikayi.

Malam Bunu Abatcha daya daga cikin 'yan gudun hijiran da suka shiga Maiduguri daga Baga yace yunwa ce ta korosu. Abinci ya yi wani mugun tsada a Bagan. Kwanun shinkafa guda daya nera 2,500 ne. Kwalbar fanta nera 250 take.

Musa Alhaji Bukar Kukawa shugaban karamar hukumar Kukawa ya karyata zargin rashin kulawa da 'yan gudun hijiran. Komawar 'yan gudun hijiran Baga ba da sanin gwamnatin jihar ba ne. Saboda haka ne sojoji suka hanasu kamun kifi ko yin noma. Wadanda suke sansanin 'yan gudun hijira da gwamnati take sane dasu ana basu abinci.

To saidai shugaban hukumar bada agajin gaggawa Injiniya Satome Ahmed yace mutanen dake ikirarin sun fito daga garin Baga basu sanar dasu a hukumance ba. Da suka shiga Maiduguri basu gabatar da kansu ga hukumar dake kula da 'yan gudun hijira ba. Maimakon haka sai suka hada baki da wasu 'yanuwansu dake cikin sansanin suka shiga. Saboda haka hukuma ta shiga ta ciresu daga sansanin domin ba'a sansu ba.

Yanzu dai an hadasu da jami'an tsaro su tantancesu. Idan basu da matsala gwamnati zata san abun da zata yi dasu.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG