Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ko NEMA a takaice Alhaji Sani Sidi ya jagoranci wata tawagar gani da ido zuwa sansanin 'yan gudun hijira dake Makohi a Yola inda wani bam ya tashi ya kuma rutsa da wasu 'yan gudun hijiran.
Tawagar ta je sansanin tare da asibitocin da aka kwantar da wadanda suka jikata. Jagoran tafiyar ya mikawa jama'an wurin sakon shugaban kasa Muhammad Buhari.
Bayan ya mika gaisuwa da jajantawar shugaban kasa da basu tabbacin daukan karin matakan tsaro yace daga wanshekare za'a kara sojoji da 'yansanda. Ya kuma gargadesu su sa ido idan akwai wanda basu yadda dashi ba su shaidawa jami'an tsaro.
Wasu 'yan gudun hijiran sun bayyanawa Alhaji Sani Sidi irin matsalolin da suke fuskanta. Suna da matsalar karancin magani kuma yayi alkawarin za'a magance matsalar. Suna da abinci amma basa samu kan lokaci. Abincin dare na kai karfe goma sha daya kafin su samu.
Alhaji Sidi ya yiwa masu son zuwa Borno alkawarin kaisu wannan makon.
Bam da ya tashi ya sa wasu 'yan gudun hijiran cikin fargaba har yanzu tare da rashin yadda da junansu.
Saboda gudun sake aukuwar abun da ya faru jami'an tsaro na cigaba da tantance 'yan gudun hijiran da aka dawo dasu daga kasar Kamaru ganin cewa can baya an samu 'yan Boko Haram a cikinsu.
Shugaban hukumar NEMA ya gargadesu da su sa ido sosai. Yace kasancewar zama dan Boko Haram ba'a rubutawa a goshi. Yayinda jami'an tsaro ke kokarin zakulosu daga jama'a su ma 'yan gudun hijiran kamata ya yi su sa ido sosai.
Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz.