Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDLEA Ta Kama Abba Kyari Sa'o'i Kadan Bayan Ta Bayyana Ta Na Nemansa


Abba Kyari
Abba Kyari

Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa ta kama Abba Kyari bayan ta bayyana neman mataimakin kwamishinan ‘yan sandar da aka dakatar, bisa zargin alaka da safarar miyagun kwayoyi.

A wata sanarwar da Maitamakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya CSP Olumuyiwa Adejobi ya fitar, ‘yan sanda sun kama DCP Abba Kyari, da wasu jami’an ‘yan sanda 4 bisa zarge-zargen samun hanunsa a cin hanci da rashawa bayan da Kakakin hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi Hukumar ya sanar hukumar ta ayyana tana neman sa bisa zargin safarar miyagun kwayoyi da cinikin hodar iblis mai nauyin kilogiram 25 yayin wani taron manema labarai a Abuja ranar Litinin.

IGP ya ba da umarnin a gaggauta mika karar zuwa NDLEA, ta kuma umarci NDLEA da binciken jami’an hukumar da ake tuhuma.

A yanzu haka rundunar ‘yan sandan Najeriya ta kama DCP Abba Kyari tare da wasu jami’an ‘yan sanda hudu bisa zarginsu da hannu dumu-dumu a cikin wasu laifuka da suka hada da hada baki, rashin gaskiya, rashin da’a, cin hanci da rashawa a hukumance da kuma yin cuwa-cuwa a kan safarar miyagun kwayoyi tare da wasu kungiyoyi masu safarar miyagun kwayoyi.

Kamen jami’an ya biyo bayan bayanan da aka samu daga shugabancin hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) a ranar 10 ga Fabrairu, 2022.

Jami’an da abin ya shafa sun hada da DCP Abba Kyari, ACP Sunday Ubuah, ASP Bawa James, ASP John Umoru (gaba daya), Inspr. Simon Agrigba da John Nuhu. A bisa haka, an mika su a yau 14 ga Fabrairu, 2022 ga hukumomin NDLEA.

Dangane da tsarin gudanarwa na rundunar, babban sufeton ‘yan sandan ya ba da umarnin gudanar da bincike mai zurfi a kan zargin. Rahoton bincike a halin yanzu ya nuna cewa an kama wasu maza biyu (2) masu saffarar miyagun kwayoyi na kasa da kasa da aka bayyana sunayensu a matsayin Chibunna Patrick Umeibe da Emeka Alphonsus, a filin jirgin saman Akanu Ibiam International Airport da ke Enugu a ranar 19 ga watan Janairu, 2022 bayan sun taso daga Addis Ababa.

Kamen ya yi sanadiyar gano wasu hoda ake zargin hodar iblis ne daga hanunsu. Rundunar ‘yan sandan liken asiri (IRT) ce ta gudanar da aikin wanda aka yi amfani da shi ta hanyar leken asiri.

Duk da cewa an mika karar da wadanda ake zargin zuwa hukumar ta NDLEA a ranar 25 ga watan Junairu, 2022, sakamakon binciken cikin gida da babban sufeton ‘yan sandan kasar ya bayar ya kafa hujja mai karfi na zargin cewa akwai yiyuwar jami’an IRT na da hannu wajen aikin da suka gudanar cewa sun tsunduma cikin wasu mu’amalarsu da kuma cin hanci da rashawa a hukumance wadanda suka saba wa ka’idojin da’a wajen mu’amalarsu da wadanda ake zargi miyagun kwayoyin da aka gano.

Mutanen biyu da aka kama masu safarar miyagun kwayoyi sun tabbatar da cewa sun hada baki da jami’an NDLEA da ke bakin aiki tare da aike musu da hotunansu kafin zuwan su domin tantancewa, ba tare da wata matsala ba, da fita daga filin jirgin ba tare da wata matsala ba tare da safarar miyagun kwayoyi.

Sun kuma kara tabbatar da cewa sun dade da wannan alakar da jami’an hukumar ta NDLEA a filin jirgin saman Akanu Ibiam tun daga shekarar 2021, kuma a cikin wannan lamari na ranar 19 ga watan Janairu, 2022, jami’an hukumar ta NDLEA sun gano su tare da wanke su kamar yadda aka saba, bayan sun karbi hotunansu da sauran bayanai kafin isowarsu Enugu, har sun kai ga hanyarsu ta fita da miyagun kwayoyi sannan ‘yan sanda suka kama su.

Rahoton binciken ‘yan sandan ya kuma tuhumi DCP Abba Kyari, wanda aka dakatar da shi bisa zarginsa da hannu a wata shari’a ta daban da hukumar binciken manyan laifuka ta kasa (FBI) ke bincike a kansa, bisa zarginsa da laifin cin hanci da rashawa a hukumance, da samun hanunsa a cinikin miyagun kwayoyi waɗanda suka saba wa daidaitattun ka'idojin gudanarwa da bincike na rundunar da kuma manyan dokokin aikata laifuka.

Dangane da sakamakon binciken kwamitin ‘yan sanda na cikin gida, babban sufeton ‘yan sandan ya bayar da umarnin kamawa tare da mika dukkan jami’an ‘yan sandan da ake tuhuma ga hukumar NDLEA domin gudanar da cikakken bincike, yayin da ake kuma fara daukar matakin ladabtarwa da ya dace.

Kafin dakatar da shi kan alaka da dan damfara Hushpuppi da aka riga aka yankewa hukuncin damfara, Kyari shine Kwamandan Hukumar Ba da Agajin Gaggawa (IRT) a ofishin leken asiri na rundunar ‘yan sandan Najeriya.

XS
SM
MD
LG