Hukumar da ke kula da gidajen gyara hali ta Najeriya, ta ce, an kama da dama daga cikin fursunonin da suka yi yunkurin tserewa bayan da wasu ‘yan bindiga suka kai hari gidan yarin Kuje da ke Abuja.
Hukumar ta kuma kore rade-radin da wasu suke yi cewa wani abu ya samu manyan mutanen da ake tsare da su a gidan yarin.
“Babu abin da ya same su, dukkansu suna nan lafiya kalau, babu abin da ya same su.” Kakakin hukumar gidajen gyara halin ta Najeriya, Abubakar Umar yay a fadawa wakilin Muryar Amurka Alhassan Bala.
Wannan gidan yari na dauke da tsohon mataimakin kwamishinan ‘yan sanda Najeriya Abba Kyari da wasu fitattun ‘yan siyasa da ake tsare da su.
A daren Talata wasu mahara da ba a fayyace ko su waye ba, suka far wa gidan yarin na Abuja, babban birnin Najeriya.
Sai dai kamar yadda kakakin hukumar gidajen yarin ya ce, sojoji sun kai dauki a lokacin harin.
“Allah ya taimake mu, mun kore su a jiyan.” In ji Umar.
Rahotanni da dama sun yi nuni da cewa daruruwan fursunoni sun tsere a lokacin harin.
Sai dai Umar ya ce, “ba gaskiya ba ne, ba wai cewa ba a samu wadanda suka tsere ba ne,” domin an kamo wadanda suka gudu, yana mai cewa suna ci gaba da tantance adadin wadanda aka kamo.
Saurari cikakkiyar hirar Kakakin hukumar gidajen yarin Najeriya da nakilin Muryar Amurka Alhassan Bala: