A cikin ‘yan kwanaki da Kamfanin mai na Najeriya wato NNPCL ya rage farashin litar man fetur daga Naira dubu 1 da 60 zuwa Naira dubu 1 da 40, kungiyar IPMAN ma ta tabbatar da cewa, mambobinta sun rage kudin nasu mai da Naira 20 har zuwa 40.
Taron zai samu halartar mutane sama da dubu 1 da suka hada da masu baje kolin hajarsu, masu zuba jari daga gwamnati da kamfanoni masu zaman kan su daga kasashen Afirka, Turai, Asiya, da Amurka.
Kasa da sa’o’i 48 da sanarwar gargadi da babban bankin Najeriya ya yi game da hanyar damfara da sunan tsarin SWFT code na tura kudi tsakanin ‘yan kasuwan kasa da kasa, masana tattalin arziki suna gani akwai mafita.
Wata babbar kotun tarayya da ke birnin tarayyar Najeriya, Abuja ta yi watsi da karar da ake tuhumar gomman kananan yaran nan da ake zargi da laifin cin amanar kasa wadanda aka tsare na kusan kwana casa’in sakamakon shiga zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa inda suka daga tutar kasar Rasha
Masana da mahukunta sun ce Hukuncin da babbar kotu ta yanke na haramtawa hukumar VIO tsarewa ko kuma cin tarar direbobin motoci a birnin tarayya Abuja, ya kawo cikas ga harkokin su na samun kudadden shiga da kuma kaiwa ga kara yawan direbobin dake saba ka’idar tuki a Abuja.
Wasu kungiyoyin ba da tallafi masu zaman kan su, sun ce har yanzu da sauran rina a kaba a garuruwan da ambaliyar ruwa ta shafa kuma al’umomin garuruwan na bukatar taimakon al’uma a ciki da wajen Najeriya.
Ga dukkan alamau har yanzu akwai sauran rina a kaba game da batun wanzuwar man fetur a Najeriya da kuma arhar shi duk da shigowar matatar man Dangote cikin harkar.
Mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya ce shugaba Tinubu yana kaunar Arewa da al'ummarta kuma dalili kenan da yasa ya bada kashi 62 cikin 100 na majalisar zartarwar sa ga 'yan arewa. Abin da ya rage shine Arewa ta hada kai domin samun ayyukan ci gaba daga wannan gwamnati.
Masana tsaro da masu sharhi a kan al’amurran yau da kullum sun gargadi gwamnati a kan mahinmancin daukan matakan da suka dace cikin gaggawa don gudun kar wata rana talakawa su cinye su, yayin da zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriya ta shiga kwana na 7.
Har yanzu ana ci gaba da zanga zangar nuna bacin rai game da tsadar rayuwa a Najeriya. A gefe guda kuma, masu fada a ji da sauran 'yan kasa na bayyana mabanbantan ra'ayoyinsu game da zanga zangar da kuma halayen wasu masu zanga zangar.
Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bukaci wadanda suka shirya zanga-zangar neman a kawo karshen tsadar rayuwa a kasa da su dakatar da duk wata zanga-zanga, domin kuwa kofar gwamnati a bude take a tattaunawa a kuma yi sulhu a samo hanyoyin kawo sauki a yanayin matsin da ‘yan kasa ke ciki a yanzu.
A yayin da aka shiga yini na biyu na zanga-zangar neman kawo karshen tsadar rayuwa a Najeriya, masu zanga-zangar sun lashi takobin ci gaba da fitowa har sai gwamnati ta saurari kokensu kuma ta biya musu bukatun da suka gabatar ko da sama da shekara daya za su shafe.
Wasu daga cikin masu zanga-zangar da suka fita dandalin zuwa Eagle Square sun fadawa Muryar Amurka cewa matakin jefa musu barkonon tsohuwa ba zai dakile su ba.
A yayin aikin hajji na bana dai, hukumar NAHCON ta kayyade kudin da maniyatta za su biya a kan dala dubu 5 da 692.25 a madadin wanda aka tsara a farko-farko na dala dubu 6 da 401.31 inda aka sami ragin dala 700 da centi 6 a bisa ana canjin naira zuwa dala a kan naira 456 a waccan lokaci.
A yayin da wasu ‘yan Najeriya ke ci gaba da korafe-korafe a kan yadda masu damfara ta yanar gizo ke ci gaba da yi mu su illa, kamfanin Meta mamallakin shafukan Instagram, Facebook da WhatsApp ya dauki matakin rufe wasu shafukan Facebook dubu 63.
Domin Kari