Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Hushpuppi: An Dakatar Da Abba Kyari Daga Aiki


Abba Kyari (Facebook/Abba Kyari)
Abba Kyari (Facebook/Abba Kyari)

Matakin ya biyo bayan tuhumar da Amurka take yi wa Kyari kan zargin ya karbi cin hanci a hannun wani dan Najeriya mai suna Ramon Abbas, wanda aka fi sani da Hushppupi, zargin da ya musanta.

Hukumar da ke kula da sha’anin rundunar ‘yan sandan Najeriya ta PSC, ta dakatar da Mataimakin Kwamishina Abba Kyari daga aiki bisa zargin karbar cin hanci.

Dakatarwa na dauke ne a wata sanarwar da kakakin hukumar Ikechukwu Ani fitar a ranar Lahadi.

Gabanin hakan, Babban Sufeton ‘yan sandan kasar Usman Alkali Baba, ya ba hukumar shawarar a dakatar da Kyari.

Matakin ya biyo bayan zargin sa da ake yi wa Kyari da karbar cin hanci a hannun Ramon Abbas da aka fi sani da Hushpuppi, wanda ke fuskantar shari’a a Amurka kan ayyukan damfara ta yanar gizo.

“Dakatarwar ta Abba Kyari ta fara aiki daga ranar Asabar 31 ga watan Yuli, 2021, har zuwa kammala binciken da ake yi bisa tuhumar da hukumar hukunta manyan laifuka ta FBI a Amurka take yi masa.”

Kwamitin da aka kafa don bincike lamarin, wanda ke da manyan jami’an ‘yan sanda hudu, zai yi aiki ne karkashin jagorancin DIG Joseph Egbunike, wanda shi ne shugaban sashen binciken manyan laifuka a rundunar a cewar wata sanarwa ta daban da Frank Mba ya fitar.

Ana sa rana kwamitin zai tattaro dukkan bayanan da suka shafi zargin da ake yi wa Kyari, ya kuma gudanar da bincike tare da ba da shawara kan matakin da ya kamata a dauka kan wannan lamari a cewar sanarwar ta Frank Mba.

A karshen makon da ya gabata, Hushpuppi ya amsa laifinsa a gaban kotun Amurka kan tuhumar da ake masa.

A kuma ranar Alhamis kotun Amurka ta ba hukumar hukunta manyan laifuka ta FBI umarnin ta kama Kyari.

Sai dai Kyari ya musanta zargin da ake masa a wani rubutu da ya yi a shafinsa na sada zumunta inda ya ce, bai taba karbar ko sisi a hannun Hushpuppi ba.

Amma ya ce ya taba masa hanya ya sayi wasu kayayyakin sa wa da kudinsu ya kai naira dubu 300.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG