Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kanin DCP Abba Kyari Ya Shigar Da Kara Kan Take ‘Yancin Kyari A Hukumar NDLEA


Abba Kyari (Facebook/Abba Kyari)
Abba Kyari (Facebook/Abba Kyari)

Kanin tsohon shugaban rundunar kai daukin gaggawa kan bayanan sirri na ‘yan sandan Najeriya DCP Abba Kyari ya shigar da kara babbar kotun tarayya ya na bukatar a ba da belin dan' uwansa.

Kanin mai suna Usman, ya shigar da karar a matsayin zabin da ya rage bayan kokarin ganin NDLEA ta ba da belin Kyari bisa hujjar kasancewar sa sanenne kuma jami’in ‘yan sanda. Bisa ga cewarsa, hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi NDLEA ta dannewa Kyari hakki bayan zarginsa da hannu a safarar miyagun kwayoyi

Usman ya bukaci alkalin kotun Inyang Ekwo ya duba ba da belin Kyari da ke tsare tun kama shi da’a aka yi a ranar 12 ga watan nan. An shigar da karar ta hannun lauya C.O. Ikena da ke nuna irin sadaukar da kai da Kyari ya yi, ya cancanci mutuntawa.

Bayanan lauyan sun nuna matsayar hukumar NDLEA ta zambaci DCP Kyari da sanya shi taka kafar barawo.

Kyari ya bukaci diyyar Naira miliyan 500 da neman gafara da ya ke bukatar NDLEA ta buga a jaridu biyu.

Alkali Ekwo ya sanya ranar larabar nan 24 ga watan Febrairu da umurtar a sanar da NDLEA halin da a ke ciki.

A wani labari da ke da alaka da wannan lauyan da ke kare Abba Kyarin Ms Ikena ta shaida wa manema labarai cewa kyari na fama da rashin lafiya na ciwon Sukari da hawan jini wanda bisa wannan hujja yasa ake neman a ba da belin shi.

Sanarwar da hukumar ta NDLEA ta yi na zuwa ne ‘yan watanni bayan da wata kotu a Amurka ta gurfanar da shi kan wata shari’ar zamba ta intanet tare da abokin harkallarsa; Hushpuppi.

Bayan sanarwar, rundunar ‘yan sandan Najeriya ta sanar da cewa an kama Mista Kyari ne tare da wasu mutane hudu na tawagar ‘yan sandan da suke aiki tare a harkar kwayoyi

Idan ba a manta ba, a ranar 14 ga watan Fabrairu ne hukumar NDLEA ta zargi Kyari hada baki da kuma aiki da wata tawagar safarar miyagun kwayoyi ta kasa da kasa.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG