Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilin Da Ya Sa Kotu Ta Ki Amincewa Da Bukatar Mika Abba Kyari Ga Hukumomin Amurka


Kotu
Kotu

A ranar Litinin ne wani alkali a Najeriya ya yi watsi da bukatar da gwamnatin tarayya ta gabatar na mika tsohon mataimakin kwamishinan 'yan sanda Abba Kyari ga Amurka domin fuskantar tuhume-tuhume masu alaka da zamba.

WASHINGTON, D.C. - Abba Kyari ya musanta cewa yana da hannu a cikin abin da wata kotu da ke Amurka ta bayyana a matsayin wani gagarumin shiri na cewa ya damfari wani dan kasuwa dan kasar Qatar sama da dala miliyan daya, wanda wani fitaccen dan damfara na Najeriya da aka fi sani da "Hushpuppi ya shirya."

Kyari ya musanta aikata laifin.

Hushpuppi
Hushpuppi

Yana gidan yari yana jiran shari’a bisa wasu tuhume-tuhume daban-daban na zargin hada baki, cin hanci da rashawa a hukumance da kuma yin katsalandan a baje koli bayan da hukumar yaki da muggan kwayoyi ta kasar ta kama shi a watan Fabrairu.

A ranar Litinin ne alkalin babbar kotun kasar, Inyang Ekwo, ya ce ba za a iya mika Kyari ba saboda wannan shari’a da ake yi a Najeriya, domin mika shi ga Amurka zai saba wa dokar kasar.

Abba Kyari
Abba Kyari

Ba mu dai samu jin ta bakin Ministan shari’a kuma babban lauyan gwamnatin kasar Abubakar Malami ba.

Kyari na daya daga cikin mutane shida da aka gurfanar da su a kan shirin zamba a shekarar da ta gabata, a cewar wata sanarwa daga ofishin mai shigar da kara na Amurka da ke tsakiyar gundumar California.

-REUTERS

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG