Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnati Za Ta Bi Tsarin Doka Wajen Zargin Da Ake Yi wa DCP Abba Kyari - Malami


Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, hagu, Abba Kyari, dama (Facebook/Instagram/Malami/Kyari)
Atoni Janar din Najeriya, Abubakar Malami, hagu, Abba Kyari, dama (Facebook/Instagram/Malami/Kyari)

Ministan shari’a kuma antoni janar na tarayyar Najeriya ya bayyana cewa, gwamnatin kasar za ta bi doka kan yiwuwar mika mataimakin kwamishinan ‘yan sanda, Abba Kyari, bisa zargin da hukumar binciken manyan laifuka ta FBI a Amurka ta yi masa kan alaka da Hushpuppi.

Wata kotun kasar Amurka dai ta ba da umarnin a kama DCP Abba Kyari ne bisa zargin alakarasa da dan damfarar yanar gizo, Ramon Abbas wanda aka fi sani da Hushpuppi a kafafen sada zumunta da ke baje kolin arzikin da ya mallaka.

Malamin ya bayyana hakan ne a wata hira da Muryar Amurka inda ya ce gwamnati za ta yi amfani da yarjejeniyar diflomasiyya tsakaninta da kasar Amurka, kuma dole ne a bi ka’idojin doka.

A cikin kwanakin baya-bayan nan ne wata kotu a Amurka ta ba da sanarwar neman DCP Abba Kyari ya je Amurka bisa zargin alaka da Hushpuppi ya ba Kyari cin hangi, zargin da yeke musantawa.

Hukumomin Najeriya sun dakatar da Kyari daga aikinsa, kuma tuni har an maye gurbinsa da DCP Tunji Disu.

Masana sha’anin tsaro dai sun bukaci a bi tsarin diflomasiyya wajen yin abin da ya kamata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG