Dakataccen mataimatin kwamishinan ‘yan sanda DCP Abba Kyari, ya ki amsa laifin safarar miyagun kwayoyi da hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa wato NDLEA ta gabatar a kan sa a gaban kotu.
A ranar litinin ne DCP Abba Kyari ya bayyana hakan a gaban wata babbar kotun tarayya dake da zamanta a birnin tarayya Abuja.
Yanzu haka ana neman Abba Kyari ruwa a jallo a kasar Amurka a bisa zargin alakarsa da dan damfarar yanar gizo, Abbas Ramon wanda aka fi sani da Hushpuppi.
NDLEA ta gurfanar da Abba Kyari a ranar Litinin tare da wasu mutane shida a gaban mai shari’a Emeka Nwite na babbar kotun tarayya da ke Abuja, bisa zarginsa da aikata laifuka takwas da suka hada da safarar miyagun kwayoyi.
Haka kuma, cikin wadanda aka gurfanar tare da DCP Kyari akwai mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ACP Sunday Ubua, mataimakin Sufeto ASP Bawa James, Insfekta Simon Agirigba, Insfekta John Nuhu, Chibuinna Patrick Umeibe da kuma Emeka Alphonsus Ezenwanne.
A yayin da sauran mutane hudu da ake tuhumarsu tare da Kyari suka ki amsa laifin da ake tuhumar su da su bayan da aka karanta musu, wadanda ake kara na shida da na bakwai, sun amsa laifuka uku da suka hada da na biyar, shida da bakwai.
A cewar hukumar ta NDLEA, tsakanin ranar 19 zuwa 25 ga watan Janairu, Kyari ya yi tu’amali da hodar ibilis mai nauyin kilogiram 17.55 inda ake tuhumar shi da laifin kawo cikas ga shari’a ta hanyar yunkurin ba da cin hancin jami’an hukumar NDLEA.
Kafin hukumar 'yan sanda ta dakatar da shi, DCP Kyari, mataimakin kwamishinan ‘yan sanda ne da ke kula da sashen tattara bayanan sirri a rundunar yan sandan Najeriya.