Jama'a sun kara fusata bayan da mutane suka kara bayarda rahoton dake cewa an kara sace wasu yara mata sama da 10 duk a yankin arewa maso gabashin Najeriya.
Jami'an 'yan sanda suna fata wani zai tuntube su da duk wani bayani da zasu kai ga samo wadannan yara.
Mai fashin bakin harkokin siyasa, Jibrin Ibrahim yace matakin da 'yan sanda suka dauka yayi latti, amma duk da haka ana maraba da shi.
Yace "na damu da yadda ya dauki 'yan sanda makonni uku, kafin su fahimci cewa sai sun bayarda wani ihisani kafin su samu damar ceto wadannan yara. Ina fata wani zai basu bayanan da zasu iya amfani dasu wajen nemo daliban," a cewar Mr. Ibrahim.
Shuwagabanni daga Chana da Amurka sunyi tayin taimakawa Najeriya wajen neman daliban, da kuma sako su.
"A tunani na, a zahiri akwai matsala babba wajen ceto wadannan yara, saboda bamu ga an dauki wani mataki mai kwari ba har yanzu, tun bayan da aka sace matan ran 14 ga watan da ya wuce. A tunanina, idan bamu da kayan aiki to babu wani abu don mun nemi taimako, amma kuma sai mun bi ahankali kar a keta diyaucin kasarmu," inji Ibrahim.