Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Nemi Taimakon Amurka Akan Tsaro


An gudanar da zanga-zanga Talata 6/5/2014 a kofar ofishin jakadancin Najeriya dake Washington, DC, kan neman da a ceto dalibai mata na Cibok da aka sace.
An gudanar da zanga-zanga Talata 6/5/2014 a kofar ofishin jakadancin Najeriya dake Washington, DC, kan neman da a ceto dalibai mata na Cibok da aka sace.

An yi zanga-zangar nemo kwato yara mata 'yan makarantar Sakandare Cibok ta jihar Borno,a kofar ofishin jakadancin Najeriya a Birnin Washington DC.

An gudanar da zanga-zanga yau a kofar ofishin jakadancin Najeriya dake Washington, DC, kan neman da a ceto dalibai mata 'yan makaratar Cibok.

A wajen gangamin ne akayi kira ga kasar Amurka da ta taimakawa Najeriya wajen nemo 'yan makarantan da aka sace makoni uku da suka shige wanda har yanzu ba labarin su.

‘Yan Najeriya mazuana Amurka ne suka yi wannan kira a wajen wani gangami da sukayi a kofar ofishin jakadancin Najeriya, a birnin Washington DC.

Masu gangamin sun kuma kara da cewa tunda gwamnatin kasar ta gasa wajen kare ‘yan kasar to su suna ganin cewa samun canjin gwamnati zai taimakawa kasar.

Wata ‘yar asalin jihar Borno a wajen gangamin mai suna Hyeladzira cewa tayi duk wannan rashin yin abunda ya kamata akan yaran don ba 'yayan shuwagabani bane kamar gwamnoni, sanatoci, ’yan majalisu ko kuma ‘yayan janar-janar bane.
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG