Jami’in yace ya sanarda sojoji dake gadin garin Cibok din, kuma ya gayawa wasu daga cikin mutanen garin su tashi su gudu.
Sojojin su kuma sun aika sakon neman dauki zuwa barikin da yafi kusa, misalin kilomita 48 daga Cibok.
‘Yan bindigan da ake zato ‘yan Boko Haram ne, sun isa garin Cibok bayan sa’o’i biyu. Rahotanni na cewa sojojin dake Cibok sunyi kokarin yakar ‘yan bindigan, amma an fi karfinsu da yawan makamai, shine daga baya suka gudu.
Dalibai mata da suka samu arcewa, sunce sun ji kararrakin harbe-harbe a kusa da inda suke, daga bisani kuma ‘yan bindigan suka shiga makarantar. Yaran mata sun zaci sojoji ne suka je kai musu dauki.
Sai daga baya, yaran mata suka fuskanci cewa mutanen dake tare da su, ‘yan bindiga ne, a lokacin da aka tattaro su, aka cire duka abincin dake ajje domin ciyar da dalibai.
Daga nan sai ‘yan bindigan suka umarci daliban su shiga motocinsu na “pick-up”, kana suka sakawa makarantar wuta.
Bayan kwashe yaran, da kuma tafiya da su har suka wuce kauyuka uku, sai daya daga cikin motocin ‘yan bindigan ta lalace. Daya daga cikin daliban da kawarta suka kubuce suka shiga daji da gudu, yayin da motar bayansu ta biyo su da fitilunta a kunne.
Wasu daga cikin daliban da suka kubuce, sun boye ne akan bishiyoyi suna jira motocin ‘yan bindigan su tafi.
Wadannan yara sun hada kawunansu, sukayi ta tafiya har suka hadu da wani mutum mai keke, wanda ya taimaka musu suka koma gida.
Misalin dalibai 300 ne yanzu ba’a san inda suke ba, kuma wanda yace shi dan Boko Haram ne, Abubakar Shekau yayi barazanar sayar da matan.