Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola da daina yiwa yammacin Afirka barazana - WHO


Margaret Chan shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO
Margaret Chan shugabar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice ta sanar jiya Talata cewa,cutar Ebola ta daina barazan a yammacin Afrika, kuma hadarin da take da shi ga kasa da kasa ya ragu ainun

Duk da yake yanzu cutar bata barazana ga lafiyar al’umma, jami’an hukumar lafiya ta duniya suna kira ga kasashen da cutar ta shafa su kula.

Suka ce, ana bukatar ci gaba da yiwa wadanda ke hulda da wadanda suka kamu da cutar ko kuma suke fama da farfadowar kwayar cutar rigakafin cutar Ebola. Abu mafi muhimmanci kuma shine, ganin al’umma sun dauki matakin gaggawa nan gaba idan aka sami bullar cutar. Hukumar ta gargadi a rage zirga zirga a wuraren da cutar ta bulla.

Hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace har yanzu akwai sababbin kamuwa da cutar kalilan a kasar Guniea, sai dai kasashen Saliyo da kuma Liberiasun shafe watanni basu sake samun wani da ya kamu da cutar ba. Kawo yanzu an sami mutane goma sha bakwai da suka kamu da cutar a kasar Guinea ba da dadewa ba, na baya bayan nan shine wanda aka samu ranar goma sha bakwai ga wannan wata na Maris.

Kimanin mutane dubu goma sha daya suka rasu tunda cutar ta bulla a watan Disamban shekara ta dubu biyu da goma sha uku.

XS
SM
MD
LG