Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

LIBERIA: An Samu Karin Wadanda Suka Kamu da Cutar Ebola


Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf
Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf

Gwamnatin Laberiya tace an samu wasu mutane biyu ‘dauke da cutar Ebola a cikin wasu al’ummar da a baya suka yi fama da cutar, lamarin da ya hairfar da fargabar cewa, mai yiwuwa cutar zata sake addabar kasar da ke Afirka ta yamma.

Jami’an kiwon lafiya na Liberia sun fada a jiya alhamis cewa, yanzu haka, mutane biyar aka tabbatar suna dauke da cutar Ebola, da suka hada da wani matashi dan shekaru goma sha bakwai da ya mutu da cutar ranar ishirin da takwas ga watan Yuni.

Wani jami’i a ma’aikatar lafiya ta Liberia John Sumo yace, ana gudanar da bincike kan wadanda aka samu da cutar na baya bayan nan.

“Yace abu guda da muke so mu jadada shine, daukar dukan matakan kariya da suka kamata.” An hakikance cewa, goggon birai da jemagu suna iya yada cutar, saboda haka muna bukatar kula kada muci naman wadannan dabbobin.”

A halin da ciki kuma, kasar Saliyo tace zata fadada dokar hana zirga zirga a yankunan da aka sami bullar Ebola. Shugaban kasar Saliyo, Earnest Bai Koroma, ya yi kira ga al’ummar kasar da ma na kasashen duniya, da kada suyi sake da cutar. Yace wannan wata fama ce da ake bukatar nasara. Ya shaidawa Muryar Amurka cewa, tilas ne kasashen duniya su ‘kara ‘kaimi wajen ganin an shawo kan cutar Ebola baki daya.

Cutar Ebola tafi tsananta a kasashen Saliyo da Guinea da kuma Liberia. Sama da mutane dubu 27 suka kamu da cutar a wadannan kasashen, yayinda sama da dubu 11 kuma suka mutu ta dalilin cutar.

XS
SM
MD
LG