Yaron dan shekara 15 da haihuwa dake zama a wani kauyen gabashin babban birnin kasar Monrovia an sameshi da kwayar cutar makon jiya ne. Iyayensa duka biyu su ma suna dauke da kwayar cutar Ebolan. Suna karbar magani a wajen Monrovia da wasu mutane uku cikin iyalansu..
Jami'an Liberiya suna sa ido akan mutane 150 da ake zaton suna dauke da kwayar cutar. Mutanen sun hada da ma'aikatan kiwon lafiya wadanda suka yi cudanya da iyalan yaron da ya rasu.
Wannan sabon barkewar cutar koma baya ne ga kasar dake yammacin Afirka saboda an wanketa daga cutar bara.
Tun 3 ga watan Satumba ba'a kara samun kwayar cutar ba a kasar. Watan Mayun wannan shekara hukumar kiwon lafiya ta duniya ta wanke kasar tas daga cutar.