Mataimakin ministan kiwon lafiyar Laberiya Mr. Tolbert Nyenswah, yau Talata ya jaddada cewa kada hankalin jama’a ya tashi. Ya ce an binne matashin bisa ka’idodin da suka kamata a bi kuma jami’an dake bin sawun wadanda matashin yayi mu’amalla dasu sun riga sun fara aiki.
Rahotanni daga kamfanin dillancin labaran AP ya nuna cewa matashin dan shekaru 17 da haihuwa ya rasu ne ranar 24 ga watan nan na Yuni.
Matashin dai ya rasu ne a garin Margibi, wanda yake nesa da inda aka saba ganin wannan cuta, watau dab da iyakokin kasar da Guinea da Saliyo, kasashe biyu da suma su ka ji jiki sosai da cutar Ebola. Mr. Nyenswah yace kwararru na kokarin gano ko matashin ya kama cutar ne a lokacin da yayi tafiya.
Garin Margibi na kusa da tashar saukar jiragen saman Monrovia, tazarar kilomita 50 a kudu da babban birnin kasar.