Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

EBOLA: A Saliyao daga Yau Zuwa Yammacin Lahadi Babu Mai Barin Gidansa


Jami’an dake yaki da cutar ebola
Jami’an dake yaki da cutar ebola

A kokarin da take yi na kawar da cutar ebola gwamnatin Saliyao zata hana mutane fita daga gidajensu daga yau har zuwa yammacin Lahadi

Mahukuntan kasar Saliyo sun fadawa ‘yan kasar su zauna gidajensu a karshen wannan mako.

Mahukuntan zasu dauki wannan matakin ne a kokarin da su keyi domin dakile yaduwar annobar Ebola wadda tuni ta lakume rayuka 3,000 a kasar.

Sanarwar ta gwamnatin kasar, tace za’a hana mutane fita daga gidajensu yau Juma’a har zuwa ranar Lahadi da yamma.

Yayinda mutane ke cikin gidajensu ma’aikatan kiwon lafiya zasu bi gida gida suna zakwulo mutanen dake dauke da kwayar cutar. Zasu kuma yi anfani da zarafin su wayar da kawunan mutane akan yadda zasu hana kwayar cutar yaduwa.

Alfred Palo Conteh shugaban cibiyar dake yaki da yaduwar cutar Ebola ya gayawa manema labarai cewa ma’aikatan kiwon lafiya ba zasu amince da duk wanda yaki basu hadin kai ba.

Cutar Ebola ta kama kimanin mutane 12,000 a duk fadin kasar. Wannan adadin ya fi na kowace kasa a yankin Afirka ta Yamma.

Kodayake an samu raguwar yaduwar cutar ‘yan watannin nan da suka gabata amma kwana kwanan nan aka sake samun mutane 33 sabbin kamu a wajejen Birnin Freetown babban Birnin kasar da arewacin kasar kusa da iyaka da kasar Guinea.

A kasar ta Guinea har yanzu ana cigaba da samun sabbin kamu yayinda cutar ta kusa barin kasar Liberiya gaba daya domin mutum daya kawai ya kamu da ita cikin ‘yan watannin nan.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG