Wata 'yar jaririya mai kwana 21 da shigowa duniya da aka san ta kamu da kwayar cutar Ebola ta murmure.
Wannan jaririyar ita ce ka karshe. Kafin ta murmure ta samu karbar jinya ne a cibiyar cutar ebola dake Conakry babban birnin kasar. Cutar ebola dai ita ce wata mumunar cutar da ta barke a yammacin Afirka da ta lakume rayukan mutane da dama.
Har yanzu akwai mutane da dama da ake sa ido a kansu a gani ko suna da alamun kamuwa da kwayar cutar. Bayan kwanaki 42 idan babu wanda ya kamu da cutar to kasar to za'a fitar da kasar daga ayarin kasashen dake fama da cutar. Kasar Guinea ta yi kusan shekaru biyu tana fama da cutar.
Jami'ar hukumar kiwon lafiya ta duniya ko WHO a takaice tace tana yiwuwa a kawo karshen ebola a kasar ta Guinea nan da lokain Kirsimati.
Kasashe biyu dake makwaftaka da Guinea da su ma suka sha fama da cutar wato Liberiya da Saliyao tuni WHO ta cire sunayensu daga kasashen da suke da cutar.
Annobar ebola da ta fara barkewa a kasar a Guinea ta kashe fiye da mutane 11,000 a Afirka ta yamma