Jami’an kiwon lafiya na Amurka sun fara rufe kananan asibitocin da suka bude a kasar Laberiya, a lokacin da cutar Ebola ta tsananta a shekarar data wuce, kamar yadda kasar ke shirin zama sahun kasashen da suka dakile mummunar cutar ta Ebola.
Kasar Laberiya dai ta yi kwana 32 ba tare da an sami wani ya kamu da cutar ta Ebola ba. Idan har kasar ta zamanto a haka har zuwa 9 ga watan Mayu, to hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO na iya bayyana kasar a matsayin kasar da ta dakile cutar Ebola.
A shekarar data wuce ne gwamnatin Amurka ta kai sojoji sama da dubu 2 domin su taimaka a yaki cutar a Laberiya, sun kuma kafa kananan asibitoci na kula da masu cutar har 15. An dai fitar da sojojin a watan Fabarairu a lokacin dacutar ta fara lafawa.
Hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO tace, kwayar cutar ta Ebola ta kashe mutane sama da 10,000 wanda yawancinsu mutanen kasashen yammacin Afirka ne da suka hada da Gini, Liberiya, da Saliyo. A ‘kalla mutane 24,340 ne suka kamu da kwayar cutar ta Ebola, tun lokacin da cutar ta fara yaduwa a kasashen yammacin Afirka a watan Disamba na shekara ta 2013.
Kasar Liberiya ce dai tafi yawan mutane da suka mutu a dalilin ‘barkewar cutar, inda da sama da mutane 4,600suka mutu.