Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akwai Sauran Aiki A Yaki Da Ebola: Inji Shugaba Obama


Jami'an jinya sanye da rigar kariya a yaki da cutar Ebola
Jami'an jinya sanye da rigar kariya a yaki da cutar Ebola

adadin masu kamuwa da cutar Ebola ya ragu da kashi casa’in da biyar bisa dari, inda ake samun mutane kalilan dake kamuwa da cutar a mako.

Shugaban Amurka Barack Obama yace duniya tayi namijin kokari a yaki da cutar Ebola, sai dai har yanzu ba a shawo kan cutar mai kisan gaske ba.

Da yake Magana kafin ganawa da shugabar kasar Liberia Ellen Johnson Sirleaf a fadar White House jiya Jumma’a, shugaba Obama yace duk da yake cutar ta kasance wani bala’I da yayi barnar gaske, yanzu an fara magance yaduwarta.

Yace yanzu adadin masu kamuwa da cutar Ebola ya ragu da kashi casa’in da biyar bisa dari, inda ake samun mutane kalilan dake kamuwa da cutar a mako.

Mr. Obama yace a ganawar da zasu yi da shugaba Sirleaf, zasu tattauna a kan yadda za a kauda sakaci yayinda cutar take rage yaduwa, da kuma yadda za a taimaka wajen habaka tattalin arzikin Liberia da kuma sake gina cibiyoyinta.

Shugaba Sirleaf tace,Amurka tayi matukar bada gudummuwa mai dorewa a Liberia ta wajen taimakawa kasarta yakar cutar Ebola.

Ta kuma yabawa al’ummar Liberia sabili da aiki tukuru wajen yakar cutar. Sai dai tace har yanzu kasar Liberia da sauran kasashen dake yankin suna cikin hadari. Tace har yanzu al’ummar kasar Liberia na cikin hadari, muddar ba a shawo kan cutar a kasashen dake makwabtaka da Liberia ba.

Hukumar lafiya ta duniya ta sanar jiya Jumma’a cewa, cutar Ebola ta kama kusan mutane dubu ishirin da hudu a Guenea da Liberia da Saliyo ta kuma kashe sama da mutane dubu tara da dari shida.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG