Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Cutar Ebola: Amurka Zata Janye Yawancin Dakarunta Daga Afirka ta Yamma


Wurin da ake kula da yara akan cutar ebola
Wurin da ake kula da yara akan cutar ebola

Yayinda cutar ebola tayi kamari a Afirka ta Yamma Amurka ta tura wasu dakarunta domin gina cibiyoyin jinya, sarafa magunguna da horas da ma'aikata

Shugaban Amurka Barack Obama zai janye galibin dakarun Amurka da aka tura Yammacin Afrika domin shawo kan cutar Ebola.

Amurka ta tura ma’aikata dubu uku domin kafa cibiyoyin jinyar cutar Ebola da kuma wadansu cibiyoyin yaki da kwayar cutar. Da yake jawabi ranar Laraba a Washington, Mr. Obama yace ganin yadda aikin dakarun ya yi nasara, dukansu zasu dawo nan da ranar talatin ga watan Afrilu,sai kimanin guda dari kawai za’a bari baya.

Yace dakaru dubu daya da goma sha biyar sun riga sun iso gida.

Shugaban kasar yace yana so a fahimci cewa, duk da yake dakarun zasu dawo gida, ba’a kammala aikin yaki da cutar Ebola ba. Yace yanzu inda aka sa gaba shine ganin babu wanda yake dauke da cutar, saboda bisa ga cewarshi, kowanne aka samu yana dauke da cutar zai sake maida hannun agogon baya.

Dakarun Amurka da za’a bari a Afrika ta yamma zasu yi aiki da sojojin Liberia da abokan kawance a lardin da kuma Amurkawa farin kaya a cigaba da yaki da cutar Ebola.

XS
SM
MD
LG