Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Liberia Ta Magance Cutar Ebola


Na'urar Gwajin Cutar Ebola
Na'urar Gwajin Cutar Ebola

Hukamar lafiya ta Majalisar dinkin duniya ta bayyana kasar Liberia a matsayin wacce ta yi nasarar kawar da cutar ebola mai kisa daga kasar.

Cutar Ebola ta hallaka mutane da dama a nahiyar Afrika ta Yamma musamman a kasar Laberiya, Saliyo da Gini. Sannan kasashen duniya na ci gaba da sa idon ganin an agaza wajen shawo kan cutar.

Wannan sanarwar ta fito ne bayan kasar Laberia ta bayyana cewa basu sami wani sabon labarin bullar cutar ba har tsawon kwanaki arba'in da biyu, wanda wannan kwanakin rubi biyu ne na lokacin kyankyasar kwayar cutar ta ebola a cikin jikin mutum.

Amma duk da haka akwai sauran cutar a cikin nahiyar Afrika ta Yamma, kamar Siraliyo da Gini makwabtan na Laberiya, wanda dukkan kasashen guda biyu sun bada rahoton kamuwa da cutar kamar guda tara a makon da ya gabata.

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG