Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shahararrun Mutane a Duniya Na Goyon Bayan Zanga-zangar ‘Yan Najeriya


Fitaccen mai wakar gambara na Amurka Kenye West, ya shiga jerin shahararrun mutane a fadin duniya dake goyon bayan gagarumar zanga-zangar kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda a Najeriya.

A wani sako da ya kafe a shinfsa na Twitter, Kenye West ya ce “Ina tare da ‘yan uwana maza da mata a Najeriya domin kawo karshen cin zarafin ‘yan sanda, dole ne gwamnati ta amsa kukan mutane.”

Zanga-zangar ake gudanarwa a biranen fadin Najeriya na zuwa ne bayan ‘yan makonni da matasa ke ta bayyana bacin ransu game da halin rashin tsaro da ake fama da su a kasar, ciki har da garkuwa da mutane domin kudin fansa da cin zarafi da cin hanci daga rundunar ‘yan sanda masu yaki da ‘yan fashi da makami da aka fi sani da ‘SARS.’

Sai dai an ci gaba da gudanar da zanga-zangar bayan da babba Sifeton ‘yan sanda Mohammed Adamu, ya sanar da wargaza rundunar SARS tare da rarraba jami’an ‘yan sandan zuwa wasu sashe.

Masu zanga-zanga a Najeriya
Masu zanga-zanga a Najeriya

Ta hanyar amfani da kalmar #EndSARS a kafafen sada zumunta, shahararrun mutane a fadin duniya sun hadu da ‘yan Najeriya a wannan kira domin kawo karshen dukkan nau’ukan cin zarafin ‘yan sanda.

Shugaban ‘yan sandan Najeriyar ya ce daga yanzu za a samar da wani dandali inda shugabannin ‘yan sandan zasu yi aiki kafada da kafada da jama'a a dukkannin matakai don sa ido a kan ayyukan ‘yan sandan.

Sai dai wannan mataki na rundunar ‘yan sandan bai yiwa wasu ‘yan kasar dadi ba, domin a yayin da ake tsakiyar wannan zanga zangar ne kuma Majalisar matasan Arewa ta aikewa da shugaba Buhari wata doguwar wasikar neman kin amincewa da soke rundunar ta SARS, tana mai cewa hakan ka iya kara tabarbarar da yanayin tsaro a yankin arewacin kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG