Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Amurka: Muna Saka Ido Kan Cin Zarafin Da Ake Wa Masu Zanga-zanga A Najeriya


Majalisar Amurka
Majalisar Amurka

Kasashen duniya na kira da a kawo karshen gallazawa da kuma kisan da ake ma masu zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS a Najeriya.

A daidai lokacin da ake cigaba da gudanar da zanga-zangar kawo karshen rundunar ‘yan sanda ta #SARS a fadin Najeriya wadda ta rikide zuwa zanga-zangar kuncin rayuwa, ake kuma ganin jami’an tsaro na dirar mikiya akan masu gudanar da zanga-zangar, kasashen duniya sun fara tofa albarkacin bakinsu akan abubuwan da ke gudana.

Shugaban kwamitin harkokin kashen ketare a Majalisar Wakilan Amurka, Eliot Engel, ya rubuta a shafin twitter na kwamitin harkokin kasashen waje na majalisar cewa, “Ina mai matukar bakin ciki akan yadda jami’an tsaron Najeriya ke amfani da alburusai akan masu zanga-zangar kawo karshen rundunar SARS.”

https://twitter.com/HouseForeign/status/1318896226163740672

Kuma ace mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka, da ofishin jakadancin Amurka a Najeriya basu yi Allah wadai da wannan munmunan aikin ba?

Haka zalika dantakar shugaban kasar Amurka karkashin jami’iyyar Demokarat, Joe Biden yayi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da jami’an tsaro su gaggauta kawo karshen wannan halin da ake ciki, na harbin masu zanga-zanga, wanda ya yi sanadin mace-mace.

Ya kara da cewa “Zuciyata tana tare da duk wadanda suka rasa ‘yan uwansu a wannan fafutukar. Amurka dole ta yi tarayya da ‘yan Najeriya masu zanga-zangar lumana, don kawo sauyi a bangaren tsaro, da kuma neman a kawo karshen cin hanci da rashawa a tsari irin na demokaradiyya.”

Dan takara Joe biden
Dan takara Joe biden

Ya kara da cewa, “Ina rokon gwamnati ta zauna da wadanda abun ya shafa, da kyakkyawar manufa don nemo bakin zaren, da magance dadaddiyar rashin jituwa a tsakanin bangarorin biyu.”

Hillary Clinton
Hillary Clinton

Haka a nata bangaren uwargidar tsohon Shugaban kasar Amurka, kana tsohuwar ‘yar takarar shugaban kasar a zaben 2016, Hillary Clinton, ta rubuta a shafinta na twitter cewa “Ina kira ga shugaba Muhammadu Buhari da sojoji su daina kashe masu zanga-zanga.”

A bangare daya kuwa, wata sanarwa da fadar shugaban Najeriya ta fitar a yau laraba dauke da sa hannun kakakinsa Femi Adesina, ta nuna cewa tuni jihohi 13 suka kafa kwamitocin da za su bincike ayyukan cin zalin da ‘yan sanda suka aikata akan ‘yan Najeriya.

A dai makon da ya gabata hukumomin Najeriyar suka rusa rundunar ‘yan sanda ta SARS, a wani mataki na yayyafawa zanga zangar ruwa, amma masu boren sun ci gaba da gabatar da wasu korafe-korafe da suke so a magance musu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG