Zanga zangar neman rushe Rundunar Tsaro ta ‘Yan Sadan SARS da aka fara a sassa daban daban a Najeriya ya canja salo a Jihar Edo dake kudancin Najeriya.
Kawo yanzu dai bayanai sun nuna zanga zangar ta kazamce a Jihar Edo dake yankin Nija Delta, ko daya ke Hukumomi a Nijeriya tuni sun rushe SARS da ake zargi da cin zarafi da wasu laifuka da dama, aka kuma maye gurbinta da SWAT,duk da haka wannan zanga zanga na dada ruruwa zuwa tashin hankali inda daruruwan matasa suka fito zanga zanga.
Gwamnatin ta Edo ta saka dokar hana fita na sa’oi ashirin da hudu biyo bayan wani hari da aka kai ofisoshin ‘yan sanda da kuma kubutar da firsunoni dake gidan yari.
Dokar ta hana fita dai a jihar ta fara ne daga litinin 19 ga watan Oktoba inda wani mai baiwa gwamnan Edo shawara akan al’amuran ‘yan arewa mazauna Edo wato Sahabi yace suna zaman dar- dar sakamakon wannan tashin hankali.
Yace, “masu zanga zanga iri biyu ne, akwai masu yin na lumana akwai kuma masu sata wadanda suke farfasa gilasan motocin mutane su amshe musu kudade kuma su hana su tafiya.”
Gwamnatin Edo dai tace hare-haren na ‘yan daba ne, kuma ‘yan dabar na neman kwace iko. Tace ba zata zura tana kallon abubuwa nata faruwa a jihar ba.
A nasu bangaren, mazauna garin na Edo sun yi kira ga gwamnatin tarayya da ta basu abinda suke bukata a huta.
Rundunar ‘yan Sandar Jihar ta tambatar da kaiwa ofisoshinta uku hare hare yayinda kwamishinan yan sandan jihar Johnson Babatunde ya bayyana cewa rundunar a tsaye take wajen ganin ta kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Saurari cikakken rahoton Lamido Abubakar cikin sauti:
Facebook Forum