Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Legas: Shelkwatar Hukumar Kula Da Jiragen Ruwa (NPA) Ta Kama Da Wuta


Hadiza Bala Usman
Hadiza Bala Usman

Wata babbar gobara ta tashi a shelkwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa ta NPA da ke Legas, a wani yanayi mai daure kai kuma a wannan marra ta zanga zanga.

Shelkwatar hukumar kula da tashoshin jiragen ruwa dake layin Marin, a birnin Legas ta kama da wuta. Har ya zuwa yanzu babu cikakken bayanin da ke nuna yadda gobarar ta kai ga tashi.

Amma alamu na nuni da cewar masu zanga-zangar kawo karshen rundunar ‘yan sanda mai yaki da ‘yan fashi ta SARS ne suka tada gobarar, wasu kuma rahotanin na nuni da cewar wasu daga cikin ma’aikatan hukumar ne suka haddasa wutar don cinma wata manufa tasu ta daban.

Hukumar Kula da Tashoshin jiragen ruwa
Hukumar Kula da Tashoshin jiragen ruwa

Tun dai da daren jiya Talata gwamnatin tarayya ta aika da jami’an ‘yan sanda yankin, don ganin masu zanga-zangar basu kai ga gine-ginen gwamnati dake yankin ba. Muryar Amurka ta yi kokarin samun Hajiya Hadiza Bala Usman, shugabar hukumar don samun karin bayani, amma hakar bata cinma ruwa ba.

Shugabar NPA, Hadiza Bala Usman
Shugabar NPA, Hadiza Bala Usman

Kana a bangare daya, rahotanni na bayyana cewar gidan mahaifiyar gwamnan jihar ta Legas, Babajide Sanwo-Olu shima yana cida wuta, amma ba a san sanadin tashin wutar ba, sai tashar motocin safara ta Bus Rapid Transit, wadda ita ma ta kama da wuta babal.

A wasu rahotannin kuma da muka samu, yanzu haka masu zanga-zanga sun kona tashar motocin bus na BRT a yankin dake Ojodu a Berger kan hanyar Legas da Ibadan, wannan tashar ita ce ta biyu da suka saka ma wuta a yau Laraba.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG