Cikin wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter, @ProfOsibanjo, ya ce, “na fahimci cewa da yawanku kun yi fushi, da mun sani mun dauki matakin gaggawa, amma muna neman afuwarku.”
Tun a makon da ya gabata Najeriya ta tsunduma cikin kangin zanga zangar neman a rusa rundunar ‘yan sanda ta SARS da ke yaki da masu fashi da makami.
Masu zanga zange na neman a ruguza rundunar ce saboda zarginta da ake yi da gallazawa jama’a - a wasu lokuta ma har da kisan kai.
A kuma ranar Litinin hukumomin kasar suka ji kiraye-kirayen ‘yan Najeriyar suka soke rundunar.
“Tare da umurnin shugaban kasa, an ruguza rundunar ta SARS, kuma babu wani mambanta da zai yi aiki cikin wata sabuwar rundunar ‘yan sanda ta musamman.” Farfesa Osibanjo ya kara da cewa a sakonsa na Twitter, wanda ya wallafa a ranar Juma’a.
Sai dai duk da hukumomin kasar sun soke rundunar suka maye gurbinta da wata sabuwa da aka wa lakabi da SWAT, har yanzu masu zanga zangar ba su janye ba.
Rahotanni daga manyan biranen kasar kamar Abuja da Legas, sun yi nuni da cewa masu boren sun ci gaba da gudanar da zanga zangar tare da rufe wasu manyan hanyoyin sufurin biranen.
Har ila yau rahotannin sun nuna cewa, masu zanga zangar sun gabatar da wasu sabbin bukatu, da suka hada da sakin mambobinsu da aka kama, karawa ‘yan sanda albashi, yi musu gwajin lafiyar kwakwalwa da dai sauransu.
Bayanai na baya-bayan sun kuma nuna cewa, an samu kishiyoyin masu zanga zangar neman a soke SARS a biranen Legas da Abuja inda aka yi arangama.
A dalilin haka kungiyar matasa ta kasar wato NYO ta kira taron manema labarai a Abuja domin janyo hankalin matasan kasar a kan su yi hattara kada abin da ta kira “wasu miyagu” su yi amfani da damar wajen cimma wata manufa ta daban.
Taron dai ya hada shugabannin kungiyoyin al’umma daban-daban a fadin kasar da ke karkashin kungiyar matasan Najeriya wato NYO, don lalubo mafita dangane da zanga zangar da aka shafe tsawon kwanaki ana yi.
Cikin wata sanarwar ta daban da mataikin shugaban kasa Osinbanjo ya fitar a taron majlaisar raya tattalin arzikin kasa wato NEC a takaice da ake gudanarwa a Iowans wata, ya ba da umurni ga gwamnonin jihohi a kasar da su dau ragamar kafa rundunar tsaro ta musaMman tare da kafa kwamiti da zai sa ido wajen kare hakkin dan adam a jihohinsu.
Ya kuma nuna bukatar duba ayyukan sabuwar sashin rundunar ‘yan sanda ta SWAT da dukkan hukumomin tsaro da ke jihohinsu har da babban birnin tarayyar kasar Abuja.
Duk hakan dai na faruwa ne a kuma daidai lokacin da a wasu yankunan arewacin Najeriya musamman yammaci aka yi zanga zangar nuna goyon baya ga rundunar ta SARS da kuma kiran a kawo karshen matsalolin ‘yan bindiga da ke addabar yankin.
Facebook Forum