Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Zanga Zangar Kyamar SARS: An Kafa Dokar Hana Fita Jihar Legas


An Kona Ofishin Yan Sanda a Legas.
An Kona Ofishin Yan Sanda a Legas.

Yayin da ake ci gaba da gudanar da zanga zanga #EndSARS a wasu sassan manyan birane a Najeriya, gwamnatin jihar Legas ta kakaba dokar hana fita ta  tsawon sa’a 24 a duk fadin jihar.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu, ya bayyana haka a shafinsa na Twitter, inda ya ce “Yanzu haka na saka dokar hana fita ta tsawon sa’a 24 a duka fadin jihar daga karfe 4:00pm na yamma na ranar 20 ga watan Oktoba. “Ba mu yarda mu ga wani ba, illa ma’aikata da suke aiki na musamman da kuma masu kai daukin gaggawa. Su kadai ne za a gani a kan tituna.”

Hakan dai ya biyo bayan wata tarzomar da ta barke, inda ake zargin wasu ‘yan zauna gari banza da kona ofishin ‘yan sanda na Orile da ke jihar.

Ko a jiya Litinin 19 ga watan Oktoba ma masu zanga zangar sun hana fasinjoji shiga filin jirgin saman kasa da kasa na Murtala Muhammad da ke jihar Legas.

Zanga Zangar EndSARS a Abuja 2
Zanga Zangar EndSARS a Abuja 2

A Abuja kuwa babban birnin tarayyar Najeriya, an gudanar da zanga zangar kashi biyu, bangare na daya na goyon bayan gwamnati yayin da daya bangare kuma ke cigaba da zanga zangar kawo karshen rundunar yan sanda ta SARS.

An tura karin jami’an ‘yan sanda jiya Litinin, domin su dawo da doka da oda a sassan birnin Abuja, bayan da masu zanga zangar suka toshe manyan hanyoyin birnin, inda daga bisani wasunsu suka hana fasinjoji shiga filin jirgin saman birnin.

Rahotannin da kafafan yada labarai suka wallafa sun nuna cewa wasu da ake zargin tsageru ne sun kai hari kan masu zanga zangar #EndSARS#, inda suka kona motoci da dama da maraicen jiya Litinin.

Lamarin dai ya faru ne a shatale-talen Kabusa da ke kusa da Apo Resettlement a Abuja, inda suka nuna hotunan motocin naci da wuta.

Zanga Zangar EndSARS a Abuja 4
Zanga Zangar EndSARS a Abuja 4

An yi arangama tsakanin masu zanga zanga a jihar Kano da wasu matasa masu kin jinin zanga zangar.

Masu zanga zangar, wadanda galibinsu 'yan yankin kudancin Najeriya ne mazauna Kano, sun fito suna rera wakar "Buhari Must Go" wato tilas Buhari ya sauka.

Sai dai sun sami turjiya daga ayarin wasu matasa wadanda suka nuna kin jinin zanga zangar, kuma nan take suka bayyana adawarsu da ikirarin masu zanga zangar, al'amarin da ya haddasa yamutsi tsakanin bangarorin biyu.

Lamarin, wanda ya wakana akan titin zuwa Tashar jirgin sama ta Malam Aminu Kano a yankin Sabon Gari, ya so ya fantsama zuwa yankunan Sarkin Yaki Road da kuma Zungero Road dukkaninsu a yankin Sabon Garin Kano.

Daga bisani, Jami'an tsaro sun shiga tsakani domin kwantar da tarzomar, wadda ta so rikidewa ta zama ta Kabilanci ko kuma ta yanki.

Koda yake wasu majiyoyi na tsaro sun fada wa wakilin Muryar Amurka a Kano cewa, Jami'an tsaro sun daidaita al'amura, amma wasu rahotanni sunce, al'amarin ya jefa tsoro a zukatan wasu daga cikin mazauna yankin, lamarin da ya sanya wasu ke guje guje a titin Zungero Road.

Amma wakilinmu na Kano ya tabbatar da cewa babu rahotan jikkata ko rasa rayuka ko kuma lalata dukiya.

Yanzu haka dai jami'an tsaro suna ci gaba da sanya ido, domin tabbatar da doka da oda a yankin da yamutsin ya wakana.

Jami'an 'yan sanda sun kawar da masu zanga-zangar #EndSARS# a jihar Gombe, bayan da matasan su ka fito tare da hawa kan titi.

Masu zanga-zangar tun da farko sun sanar da za su shiga zanga-zangar da ke neman zama ta kasa gaba daya, sun taru a muhimmiyar mashigar Gombe daga Bauchi da aka fi sani da MIL 3, wanda yanzu ake kira, "Rainbow round-about" inda su ka fara jawo tsaikon motoci.

A daidai lokacin rubuta wannan labari, an girke motocin 'yan sanda a mashigar don hana cigaba da zanga-zangar.

Za a iya cewa yunkurin yin zanga-zangar a Gombe ka iya shafar wasu sassan jihohi 6 na arewa maso gabas don zaman jihar a tsakiyar sauran jihohin da kuma zama cibiyar kasuwanci.

Haka nan jihar ta zama tudun mun tsira ga 'yan gudun hijira daga jihar Borno lokacin da fitinar Boko Haram ta ta'azzara.

A jihar Kaduna, wadanda suka shirya zanga zangar sun ce sun dakatar da ita saboda irin yadda suka ga wasu bata gari sun shiga cikin masu zanga zangar a wasu jihohi da ma babban birnin tarayya Abuja, inda suka rinka sace sace da fashe fashe da kuma kone kone.

Daraktan gudanarwa na gamayyar kungiyoyin mutanan Arewacin Najeriya, Aminu Adam, ya ce sun dauki wannan matakin ganin irin abubuwan da suka biyo baya, inda wasu suke amafani da zanga zanga da suka yi ta kwanaki biyar, ta neman a kawo karshen rashin tsaro a yankin Arewa wanda, ake kashe kashen mutane da satar su domin neman kudin fansa.

Ko a jiya Litinin, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi kira ga masu zanga zangar da kada su bari bata gari su shiga cikinsu don su tada zaune tsaye.

Suma gwamnonin jihohi 36 na kasar sun yi kira ga masu zanga zanga da su yi taka tsantsan, suna masu cewa ya kamata a kawo karshen zanga zangar.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko wane mataki gwamnati za ta dauka a kan masu zanga zangar.



Facebook Forum

XS
SM
MD
LG