Duk da cewa gwamnatin Najeriya ta dauki matakin soke rundunar ta SARS har yanzu matasan na ci gaba da gudanar da zanga-zanga inda suka rufe manyan tituna da ke zuwa ko fitowa daga filayen jirgin saman guda biyu, lamarin da ya haifar da cikas wajen sauka da tashin jiragen sama da kuma zirga-zirgar ababen hawa.
Wani kamfanin jiragen sama ya bayyana cewa jirgi daya ne kadai ya samu tashi daga filin jirgin saman kasa-da-kasa da ke Lagos zuwa birnin Abuja a lokacin, abinda ya sa fasinjoji da yawa yin cirkocirko suna jiran tashi ko saukar jiragen.
Wasu malamai da lamarin ya rutsa da su a filin jiragen sun nuna rashin jin dadinsu akan yadda zanga-zangar ke shafar al’amuran yau da kullum sun kuma bukaci gwamnati ta dauki matakan da suka dace wajen kawo karshen wannan matsalar idan ba haka ba lamarin na iya daukar sabon salo.
Rahotanni da hotunan bidiyo sun nuna yadda masu zanga-zangar suka fara kai hari kan jami’an ‘yan sanda su kuma suna arcewa tare da barin motocinsu akan manyan titunan birnin Lagos.
Ga rahoton Babangida Jibrin cikin sauti.
Facebook Forum