Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashin Hankali: An Dakatar Da Komai A Jihar Legas Na Tsawon Kwanaki 3


Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.
Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo-Olu.

Gwamnatin jihar Legas ta soke duk wasu al'amuran yau da kullum na tsawon kwanaki uku a jihar, yayin da ta ke nazarin abin yi game da tashe-tashen hankulan da ke faruwa.

Kasancewar yanayin rashin tabbas da ke a jihar Legas, da ma Najeriya baki daya, gwamnan jihar LEGAS, Babajide Sanwo-Olu, ya bada umurnin dakatar da duk wasu ayyukan gwamnati a jihar na tsawon kwanaki uku.

Ayyukan da suka shafi fannin tsaro da masu gudanarwa kawai za su cigaba, cikin umurnin za a saukar da tutar kasa a duk ofisoshin gwamnati zuwa kasa, na tsawon wadannan kwankin 3. Gwaman ya sanar da hakan a lokacin da yake magana ta kafar talabijin yau Laraba.

Gwamnan ya umurci a kafa kwamiti mai mutane 5 da za su binciki abun da ya faru, kana wanda zai jagoranci kwamitin zai zama soja wanda ya yi murabus a mutakin Janar. Ya ce rahoton kwamitin kuma za a gabatar da shi ga Shugaban kasa nan da makonni biyu.

Ya kara da cewa “Tabbas ina iya cewa muna samun nasara tare, duk da cewer abubuwa na tafiyar hawainiya, bisa dalilin rashin shugabanci ta bangaren masu zanga-zangar kawo karshen rundunar ta SARS.”

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG