Gwamnatin jihar Edo a Najeriya ta sanya dokar hana zirga-zirga na sa’o’i 24 a yau daga karfe 4 na yamma, har sai baba ta gani a jihar.
A wata sanarwa, sakataren gwamnati jihar Osarodio Ogie ya ce matakin ya zama dole, biyo bayan ayyukan tashin hankali a kan jama'a, da ofisoshin gwamnati a jihar, da wasu ‘yan tada-zaune tsaye suke yi da sunan kawo karshen rundunar SARS.
"Duk kuwa da cewar gwamnatin jihar na goyon bayan ‘yan kasa su gudanar da zanga-zangar lumana, amma wannan ba zai zama dalili da zai sa gwamnati ta zura ido ana cin zarafin wasu ba" a cewar Ogie.
Ya kara da cewa gwamnati ba za ta bari wasu tsiraru su rinka daukar doka a hannunsu ba.
Dokar ta umurci a rufe makarantu, kasuwanni, sannan jama’a da suke cikin zullumi sai su nemi mafaka.
Ya ce ana bukatar iyaye su ja kunnen ‘ya’yansu, a kan bin doka da oda, da mutunta dokar zama a gida.
"Hakki ne da ya rataya a kan gwamnati na kare jama’a da dukiyoyin su, kana da tabbatar da an bi doka da oda, don haka duk wanda aka samu a waje ya karya dokar, za’a hukunta shi dai-dai da tanadin doka", a cewar sanarwar.
Facebook Forum