Wasu masu nazari harkokin siyasar Nigeria da wasu 'yan siyasa sun fara tofa albarkacin bakinsu akan wasikar da tsohon shugaba Olusegun Obasanjo ya rubutawa Bamanga Tukur, shugaban jam'iyar PDP. Wakilin sashen Hausa a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari ne ya zanta da su.
Tun lokacin da tsohon shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaban kasar wasika a ka ta kai ruwa rana da ra'ayoyi daban daban amma daga bangaren gwamnonin PDP shuru ka ke ji kamar an shuka dusa.
Masu kula da harkokin tsaro a Najeriya sun ce babban abinda ya fi tayar musu da hankali shi ne ikirarin da tsohon shugaban yayi cewa gwamnatin shugaba Jonathan tana horas da wasu makasa
Kungiyar hada kawunan 'yan arewa ta mayar da martani game da kalamun Sanato Hanga kan wasikar da Obasajo ya rubutawa shugaba Jonathan inda tana ganin kamar an sayeshi ne
Sanato Hanga ya Caccaki Obasanjo Kan Wasikarsa
Wasikar da Obasanjo ya rubutawa shugaban kasar Najeriya Jonathan ta kunshi abubuwa da yawa masu ban tsoro da sosa rai. Tabarbarewar tsaro da gaza kawar da barazanar Boko Haram na ciki.
Yayin da mutane ke furuci kan wasikar da Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan shi kuwa Abubakar Dangiya kashedi ya yiwa arewa
Jiya kafofin labarai a Najeriya suka bayyana wasikar da tsohon shugaba Obasanjo ya rubutawa shugaba Jonathan mai shafi 18 a bainar jama'a inda ya tabo batutuwa da yawa kuma masu mahimmanci
Idan da 'yan Najeriya na shakkun akwai baraka tsakanin Obasanjo da Jonathan, wasikar da Obasanjo ya rubutawa Jonathan yana masa kashedin kada ya shiga takarar 2015 ta kawar da duk wasu shakku.