WASHINGTON, DC —
Kungiyar hada kawunan 'yan arewa ko Arewa People Unity Forum a turance ta nisanta kanta da sukar da Sanato Hanga ya yiwa tsohon shugaba Obasanjo kan wasikar da ya rubutawa shugaban Najeriya Goodluck Jonathan.
Shugaban kungiyar Alhaji Adamu Aliyu ya ce sukar da Sanato Rufa'i Hanga ya yiwa tsohon shugaban kasa kwatakwata bata dace ba. Ya ce maganganun da Sanatan ya yi abun mamaki ne sabo da ya fito karara yana kare shugaba Jonathan. Har ma ya ce abubuwan da Obasanjo ya yi lokacin mulkinsa sun fi na Jonathan. Ya ce duk mai hankali idan ya dubi maganganunshi ya san ba gaskiya ba ne. Ya ce kuma shi Obasanjo ya fada ne tsakaninsa da Allah. Ya ce ko ta yaya Obasanjo ya fi Hanga son Jonathan domin shi ya kawo shi kan mulki. Kasancewar haka bai kamata Sanata Hanga ya fito yana irin maganganun da ya yi ba.
Idan Sanato Hanga bai manta ba shi kansa dan adawa ne. Yanzu kuma ya fito yana zagin mutanen arewa. Alhaji Adamu Aliyu ya ce cikin arewar da Sanata yake zagi akwai iyayensu da 'ya'yansu da 'yanuwansu. Sanata Hanga ya ce 'yan arewa wawaye ne wai ba zasu lura da irin wadannan maganganu zasu haifar ba sai daga baya. Kuma wannan ba gaskiya ba ne. Ya ce kada Sanato Hanga ya manta a shekarun baya sun sameshi su daidaitashi da 'yanuwansa 'yansiyasa abun ya zama bakar gaba. Sun fada masa a matsayinsa na dan siyasa yakamata su hada kawunan alumma ne ba su raba ba sabo da gudun tashe-tashen hankali.
Isa Ikara nada karin bayani.