Wani tsohon jami’in tsaron farin kaya a Najeriya, Mr. Abraham Jindo, yace babban abin lura shi ne cewa wannan maganar fa ba wai ta fito ne daga bakin wawa ba, ta fito ne daga bakin mutumin da yayi shugabancin Najeriya sau biyu, ya jagoranci rundunar sojojin kasar baki daya, kuma ya san yadda abubuwan kasa ke gudana.
Yace babban abin tayar da hankali shine zargin da Obasanjo yayi cewa shugaba Goodluck Jonathan ya tanadi wasu makasa ana horas da su domin su karkashe ‘yan adawa. Yace idan har hakan ya tabbata gaskiya, to Najeriya tana cikin wani mummunan hadari.
Shi ma masanin tsaro Dr. Abdullahi Bawa Wase, yace biri yayi kama da mutum, domin akwai hujjojin da zasu iya karfafa maganar tsohon shugaba Obasanjo.
Sai dai kuma, wani jigon jam’iyyar PDP a Adamawa, Alhaji Yayaji Gombe, yace zancen na Obasanjo zancen kawai ne domin kuwa babu wanda ya tsunduma kasa cikin masifa kamar sa. Yace yarfiyar siyasa ce, kuma neman bata suna.
Ga rahoton da Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Yola.