Yayin da yake mayar da martani dangene da wasikar da Olusegun Obasanjo ya rubutawa shugaba Goodluck Jonathan ya ce abubuwa uku ko hudu suka sa ya rubuta wasikar. Ya ce ba'a yi da shi a gwamnati mai ci yanzu. Ba'a saurarensa. Kuma dama shi mutum ne mai kishi da jin kyashi. Idan aka duba tarihinsa babu wata gwamnati da Olusegun Obasanjo bai zarga ba abun da ya kama tun daga kan Shagari har zuwa 'Yaradua. Yanzu ya farma Goodluck Jonathan domin ya tona asirinsa da na APC. Yana son ya tona asirin APC ya nuna cewa mutanen dake cikin jam'iyyar ba waliyai ba ne. Yana son a san munafukai ne.Ya rubuta wasikar ne ya kunna wuta domin a tarwatse.
Sanato Hanga ya ce buya yake yi domin yana da wata manakisa da ya shirya. Ya ce a duk fadin kasar Najeriya babu wata shiyya da tafi kudu maso yamma, wato shiyar Obasanjo cigaba. Idan da zata zama kasa mai zaman kanta yanzu to a duk fadin Afirka watakila Afirka Ta Kudu kadai zata fita arziki. Ya yi masu tashar makamashi ta zamani guda biyar cikin shidan da ya yi a kasar. Kuma kawo yanzu dukansu na aiki amma na koina a kasar basa aiki. Ya gyara masu harkar gona. Yanzu sun fi koina a Najeriya kayan abunci. Sun fi kowa harkar ilimi. A Legas ya shirya za'a gina sabon birnin gefen teku.
Kwana kwanan nan Fani Kayode ya soma zage-zage yana cewa a ware, wato kowa ya kama hanyarsa. Sun gina kansu. Basa talauci. Kashi tamanin bisa dari na arzikin kasar na wurinsu. Sabo da haka munafunci ne domin ya zunguro masifa idan ma kasar zata tarwatse ta tarwatse domin su sun yi gaba.
Duk masifar da Goodluck Jonathan ya keyi bata kai kashi daya cikin uku na abubuwan da Obasanjo ya yi ba. Duk abun da Jonathan yake yi har yanzu bai cire wani gwamna dole ba. Haka kuma bai ki amincewa da hukuncin kotun kolin kasar ba sabanin yadda Obasanjo ya yi lokacin da yake mulki. Misali hukuncin da kotun koli ta tsayar kan Ararume a jihar Imo Obasanjo ya yi watsi da shi. Haka ya hada 'yan bada suka cire gwamna Ngige daga mulki karfi da yaji. Haka ya yi anfani da mutum biyar a Filato suka cire dan takara. Ya kona garuruwa biyu, Zakibiam da One
A lokacin Obasanjo a ka karya wa 'yan arewa kadarori a Legas da ma arewa bayan an kashe 'yan arewa da dama.
To ko me yasa Obasanjo ya juyawa Jonathan baya ganin shi ne ya kawo shi mulki? Sanato Hanga ya ce ya yi hakan ne domin Jonathan ya takashi. Ya kori 'ya'yan Obasanjo a wasu jihohin Yarbawa. Inda za'a dawo da yaransa cikin jam'iyyar su wala duk wata magana da ya tayar zata mutu.
Dangane da ko gaskiya ne Jonathan na horas da wasu 'yan banga domin su bi suna karkashe 'yan hamayya Sanato Hanga ya ce a matsayin Obasanjo yana da hanyoyin da zai san abun da gwamnati ke yi. Sai dai a ce Allah ya kiyaye.
Ga cikakken rahoto.