Kullum yana yiwa 'yan arewa hannunka mai sanda cewa a tsaya a dubi Obasanjo da irin abubuwan da yake fada. Ya ce wanene ya kawo marigayi Umaru 'Yaradua da shi Jonathan? Kowa ya san wanda ya kawo su. To yau idan ya ce Jonathan bai iya ba yaushe ya san Jonathan ba zai iya rike kasar ba. Sabo da haka yakamata mutane su yi la'akari da wannan. Ya san Umaru 'Yaradua bashi da lafiya amma ya kawo shi. Jonathan ba shi bane yakamata ya zama mataimakin shugaban kasa. Tsohon gwamnan Rivers Peter Odili aka zaba amma Obasanjo ya canza ya ba Jonathan. Me ya sa Obasanjo ya yi hakan?
Wasikar da Obasanjo ya rubuta tamkar akwai lauje cikin nadi ne. Obasanjo yana fada kada Jonathan ya tsaya takarar 2015, amma shi mene bai yi ba a kasar? Shi Obasanjo ya so ya yi takara ta uku. Kuma abun tambaya nan shi ne wasikar da ya ce ya rubuta ya baiwa Janaral Babangida da Janaral Abdulsalami da Janaral Danjuma amma me ya sa bai ba Janaral Gowon ba? Don haka yakamata mutane su duba akwai lauje cikin nadi. A tsaya a dubi abun da idon basira tukunna.
Duk maganar cewa a dubi dimokradiya a kaucewa cin hanci yakamata a duba irin mulkin da Obasanjo ya yi. Idan mutum irin Obasanjo wanda ya yi mulkin kama karya ya bunkasa cin hanci da rashawa yau ya ce cin hancin ya yiwa kasar katutu to abun tsoro ne. Batun cewa gwamnati ta kasa yakamat a tsaya a yi tunane. Gwamnati ta tsaya ta yi la'akari.
Ga karin bayani.