To sai dai abun da ya daurewa 'yan Najeriya kai shi ne kawo yanzu babu daya daga cikin gwamnonin PDP da ya fito ya ce uffan. Kowanensu ya kama bakinsa ya rike tamkar an zuba masu ruwa a bakunansu. Wasu 'yan Najeriya suna tambaya ko kin yin maganarsu nuni cewa abubuwan da Olusegun Obasanjo ya rubuta babu daya da ya damesu ko ya shafesu. Ko kuma suna ganin maganar tsakanin shugabannin ne su biyu? Wasu sun ce sanin kowane cewa gwamnonin su ne suke ikirarin tabbatar da cewa kasar ta dunkule ta zama daya, tsintsiya madaurinki daya. Idan ko da gaske suke yi to ya kamata su fito su ce wani abu game da wasikar.
Mukamin gwamnoni da martabarsu sun fi karfin su yi shiru kan wasikar sai dai idan suna shakkar kada daya daga cikin shugabannin ya saka su gaba domin an ce tsohon shugaban nada hannu wajen tabbatar da darewar wasunsu kan karagar mulki. Shi kuma shugaba Jonathan duk wanda ya sokeshi ko dai a kama 'ya'yansa ko kuma shi kansa a shiga bincikensa.
Dr. Abubakar Sadiq mai sharhi a kan harkokin yau da kullum ya ce idan da akwai wani wanda zai iya magana kan wasikar Obasanjo yana cikin wadanda suka bar jam'iyyar PDP suka canza sheka zuwa APC. Gwamnonin PDP da suka rage ba wadanda suka damu da al'umma ba ne. Wasu ma cikinsu ba zabensu aka yi ba an dai dorasu ne. Sabo da haka kowa yana da bunu a gindinsa. Wasu ma idan an zagaya jihohinsu za'a samu suma suna yin abubuwan da aka zargi Jonathan da yi.
Sai dai Gali Sule ya ce babu abun da gwamnonin zasu ce domin abubuwan da suka damesu aka fada don haka murna suke yi da farin ciki. Ya ce idan ka fadawa mutum abubuwan dake damunka ya fito ya fadawa duniya ba abun da zaka yi sai dai ka ji dadi. Babu dalilin da zai sa su fito su yi magana sai da su cika da murna.
Ga karin bayani.