A cikin wasikar Obasanjo ya nuna takaicinsa na yadda a ka bar cin hanci da rashawa da satar kudin jama'a ta kowane hali suka zama abun kawa a kasar karkashin shugabancin Jonathan, musamman a harkokin gwamnati. Haka ma wasikar ta bayyana takaicin tsohon shugaban kasar yadda jam'iyyar dake gwamnati ke marawa 'yan adawa baya har ma ya bayar da misalai a cikin wasikar.
Har wayau wasikar ta ce ana ganin laifin shugaban jam'iyyar ta PDP to amma da bazar gwamnati ce yake rawa. Wasikar ta cigaba da cewa idan an ga laifin barawo shi mai bin sawu ba za'a kyaleshi ba. Kana wasikar ta ce kada shugaba Jonathan ya manta fa sun cimma matsaya cewa wa'adi guda ne zai yi na mulki.
To sai dai wani lauya mai zaman kansa Mr. G. Ogunniyi da aka tambayeshi ko me zai ce game da wasikar ya ce da shi ne shugaban kasa zai kai wasikar majalisar kasa da ta kunshi tsoffin shugabannin kasa da manya-manya shugabannin sojoji da masu fada a ji domin su warware takaddamar domin kada a jefa Najeriya cikin wani halin kakanikayi bayan damuwar da kasar ke ciki yanzu.
Da aka ce maganar matsalar PDP ce sai ya ce tafi karfin PDP yanzu. Ta zama ta kasa gaba daya domin batutuwan da wasikar ta ambato sun wuce PDP domin batutuwa ne masu karfi. Ya ce ba batu ba ne da hadiman shugaban kasa zasu sa baki ba.
Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.