Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masana Harkokin Tsaro Sun Ce Akwai Karatun ta Natsu a Wasikar Obasanjo


Tsohon shugaba Obasanjo
Tsohon shugaba Obasanjo

Wasikar da Obasanjo ya rubutawa shugaban kasar Najeriya Jonathan ta kunshi abubuwa da yawa masu ban tsoro da sosa rai. Tabarbarewar tsaro da gaza kawar da barazanar Boko Haram na ciki.

Tabarbarewar tsaro da gaza shawo kan kungiyar Boko Haram da sace-sacen da na hannun daman shugaban kasar ke yi na cikin abubuwan da tsohon shugaba Obasanjo ya tabo.

A nashi tunanen idan ba'a yi gyara cikin gaggawa ba to sojoji na iya dawowa kan mulki su kawar da shirin dimokradiya. Idan kuma ba'a ci sa'a ba za'a sake samun shugaba kamar Janaral Abacha. Kai kasar ma na iya wargajewa gaba daya.

To kamar yadda ake zato 'yan Najeriya sun soma mayar da martani kan wannan wasikar caccakar gwamnatin Jonathan. Masana harkar tsaro suna ganin akwai abun lura da ma karatun ta natsu a wasikar. Mr. Abraham Jindo wani tsohon jami'in tsaron farin kaya a kasar Najeriya ya ce magana mai mahimmanci ta fito daga bakin wanda ya taba zama shugaban kasa. Ya ce abun da ya fi damunsu a cikin wasikar shi ne batun wai shugaba Jonathan yana kebe wasu yana horas da su domin su kashe 'yan adawa. Ya ce idan haka ne kuma gaskiya ce to ko kasar tana cikin wani mugun hadari.

Haka ma Bawa Abdullahi Wase ya ce akawai abun dubawa a kalamun tsohon shugaban kasa kuma tsohon jami'in tsaro. Maganar da Obasanjo ya yi ya ce sun dade suna yi . Ya ce ya yadda da abun da Obasanjo ya fada dari bisa dari domin yana da hujjoji da suka sa ya yadda da maganar Obasanjo. Ya ce kada a manta Obasanjo ya yi mataimakin shugaban kasa a soja kana ya zama shugaban kasa na soja kafin ya zama shugaban kasa na farar hula har tsawon shekara takwas. Bugu da kari babban jami'in tsaro ne wanda janaral ne a soji ba ma na kujera ba amma wanda ya ga yaki, ya kuma yi yaki.

To sai dai kuma ga mutane kamar su Alhaji Yahaya Gombi wani jigo a jam'iyyar PDP a jihar Adamawa na ganin wasikar nada wata manufar siyasa da yunkurin bata suna. Ya ce ai babu wanda ya tsunduma kasar cikin matsala irin Obasanjo. Yau ne zai ce Jonathan bai iya mulki ba ya kasance mai laifi a gareshi. Idan shi shugaba ne na gaskiya a matsayinsa na tsohon shugaban Najeriya, a matsayinsa kuma na janaral mai ritaya kamata ya yi ya kawo kalamun da zasu kawo kwanciyar hankali ba wadanda zasu harzuka 'yan Najeriya ba. Shi Obasanjo ya manta lokacin da yake so ya zarce yayin da yake kan mulki?

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:48 0:00
Shiga Kai Tsaye
Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG