Rahotonni na bayyana cewa, kamfanin albarkatun man fetur na Najeriya NNPCL ya katse cinikayyar sayan albarkatun mai da kudin Naira dake tsakaninsu da matatun cikin gida, hadi da matatar mai ta Aliko Dangote
Gwamnatin Najeriya ta fara tantance wadanda aka mika sunayensu fiye da 100 da za su jagoranci ma’aikatun diflomasiyyarta, inda ake sa ran za a nada ‘yan diflomasiya nan ba da dadewa ba, watanni 18 bayan da shugaba Tinubu ya dakatar da dukkan jakadun kasar, a cewar wata majiya mai tushe
Harin dai ya yi sanadiyar kashe dan sa kai guda daya tare da jikkata wasu biyu, sannan suka yi awon gaba da manyan bindigogi biyu na soja.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu UNMISS ta ce tawagarta na kokarin ceto wasu sojojin Sudan ta Kudu daga wani yankin a lokacin da aka yi wa jirginsu mai saukar ungulu luguden wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikacin jirgin tare da jikkata wasu mutane biyu.
A cewar Lawal, zaman lafiya na dawowa a hankali a jihar ta Zamfara da ke yammacin arewacin Najeriya wacce ta jima tana fama da hare-haren barayin daji.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 70, ya bar 'ya'ya fiye da 40. An kuma gudanar da jana'izarsa a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025, inda dubban mutane daga ciki da wajen jihar suka halarta domin karramawa da yi masa addu'a.
Sanarwar na zuwa ne bayan da ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate ya bukaci dukkanin matakan gwamnati 3 su shigar da matasan cikin ma'aikatansu domin tallafawa aikin kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa.
Manufar matakin ita ce karfafa hanyar samu da rage tsadar kayayyakin bukatu da ayyukan kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.
Hakan ya biyo bayan binciken da kwamitin majalisar a kan da'a da alfarma da bin dokokin zaman majalisa ya gudanar, wanda ya same ta da laifin saba dokokin majalisar dattawan.
Yayin da dalibai a wadannan jihohin arewa hudu ke ci gaba da hutu, takwarorinsu na sauran jihohin kasar na ci gaba da zuwa makaranta suna karatu, su kuwa 'yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan batun inda suke kallonsa ta fuskoki mabambanta.
Abin da ya dauki hankali a wannan dambarwa shi ne a karon farko, shi da kansa Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci zaman Majalisar a lokacin da Natasha ta gabatar da takardar korafin.
Hukumar zaben Ribas mai zaman kanta (RSIEC) ta tsayar da ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa domin gudanar da sabon zaben kananan hukumomi a jihar.
Domin Kari
No media source currently available