Shugaban Sudan ta Kudu ya yi kira da a kwantar da hankula, ya kuma yi alkawarin kasarsa "ba za ta koma yaki ba," bayan da aka kai hari kan wani jirgin sama mai saukar ungulu na Majalisar Dinkin Duniya tare da kashe wani ma'aikacin jirgin a yayin aikin ceto a ranar Juma'a.
Yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin shugaba Salva Kiir da mataimakin shugaban kasar Riek Machar na fuskantar barazana a 'yan makonnin da suka gabata sakamakon arangamar da dakarun kawancensu suka yi a jihar Upper Nile da ke arewa maso gabashin kasar.
Hukumar Majalisar Dinkin Duniya a Sudan ta Kudu UNMISS ta ce tawagarta na kokarin ceto wasu sojojin Sudan ta Kudu daga wani yankin a lokacin da aka yi wa jirginsu mai saukar ungulu luguden wuta, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikacin jirgin tare da jikkata wasu mutane biyu.
An kashe wani Janar na sojojin Sudan ta Kudu da wasu jami'ai a wurin aikin ceton, a cewar wata sanarwa da UNMISS ta fitar, inda ta ce lamarin na iya zama laifin yaki.
Kiir ya yi kira ga 'yan kasar da su kwantar da hankula, yana mai cewa: "Na sha fada akai-akai cewa kasarmu ba za ta koma yaki ba. Kada kowa ya dauki doka a hannunsa."
Ya kara da cewa "Gwamnatin da nake jagoranta za ta shawo kan wannan rikicin. Za mu tsaya tsayin daka kan turbar zaman lafiya."
Sudan ta Kudu, kasa mafi karancin shekaru a duniya, ta kawo karshen yakin basasa na shekaru biyar a shekarar 2018 tare da yarjejeniyar raba madafun iko tsakanin abokan hamayyar, Kiir da Machar.
Dandalin Mu Tattauna