Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Ba Da Umarnin Daukar Ma'aikatan Lafiya 774 Aiki

Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya
Shugaban Najeriya, Bola Tinubu, a ranar Ma'aikata ta Duniya

Sanarwar na zuwa ne bayan da ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate ya bukaci dukkanin matakan gwamnati 3 su shigar da matasan cikin ma'aikatansu domin tallafawa aikin kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa.

Shugaba Bola Tinubu ya ba da umarnin daukar aiki ta kai tsaye ga ma'aikatan shirin kiwon lafiyar Najeriya 774.

Shugaban kasar ya bayyana hakan ne yayin kaddamar da shirin a Abuja, fadar gwamnatin Najeriya.

Da ya ke jawabi ga matasan da aka dorawa alhakin kula da cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko a fadin kananan hukumomin Najeriya 774, Tinubu ya ayyana cewar "an daukeku aiki", yana musu bushara da samun gurbin aiki bayan kammala wa'adinsu na shekara guda.

Sanarwar na zuwa ne bayan da ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate ya bukaci dukkanin matakan gwamnati 3 su shigar da matasan cikin ma'aikatansu domin tallafawa aikin kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa.

An tsara shirin kiwon lafiyar Najeriya ne da nufin samar da sauye-sauye masu ma'ana ta hanyar samar da kirkire-kirkire a bangaren lafiya, inda aka zabo ma'aikatan daga cikin wadanda suka nemi aikin su 359,000 a bisa cancanta.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG