A yau Alhamis, Majalisar Dattawan Najeriya ta dakatar da Sanata mai wakiltan Kogi ta tsakiya, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan har na tsawon wattani 6 a kan laifin kin amincewa da kujerar da aka ba ta a zauren Majalisar.
An kwashi lokaci mai tsawo ana muhawara kan batun amma ba a ce komai ba kan zargin cin zarafi da ta yi wa Shugaban Majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio.
Hakan ya biyo bayan binciken da kwamitin majalisar a kan da'a da alfarma da bin dokokin zaman majalisa ya gudanar, wanda ya same ta da laifin saba dokokin majalisar dattawan.
A cewar shawarwarin kwamitin da shugabansa, Sanata Neda Imaseun ya karanta, dakatarwar Sanata Natasha za ta fara aiki ne daga ranar 6 ga watan Maris da muke ciki.
Ya kuma ba da shawarar rufe ofishinta, sannan za'a hanata shiga harabar ginin majalisar a lokacin dakatarwar haka kuma za'a janye albashinta da na hadimanta.
Har ila yau kwamitin ya ba da shawarar haramta mata wakiltar Najeriya a kowane irin mataki na hukuma a matsayinta na sanata a lokacin dakatarwar.
Me yiyuwa sai 'yar majalisar ta gabatar da rubutacciyar wasikar neman gafara kafin majalisar dattawan ta sake nazari a kan dakatarwar tata, a cewarsa.
Yayin zaman majalisar a yau, Sanata Natasha Akpoti Uduaghan ta sake mika wa Majalisar Dattawa takardar korafi kan zargin da ta yi wa Shugaban Majalisar, Godswill Akpabio, cewa ya ci zarafinta, bayan da Shugaban Kwamitin jin koke-koke da kula da da'a, ladabi da kare hakkokin 'yan Majalisar, Neda Imasuen ya yi watsi da takardar korafin, kuma ya ba da hujjojin daukan wannan mataki a jiya Laraba
Sanata Godswill Akpabio ya musanta zargin inda yace bai taba yi mata wani abu na cin zarafi ba, kuma shi bai taba yi wa wata mace irin wannan cin zarafin ba.
Akpabio ya ce yana girmama mata domin yana da mata da 'ya'yansa hudu, kuma dukkan su mata ne.
Saboda haka shi bai ci zarafin kowa ba kuma ba zai ci zarafin kowa ba.
Dandalin Mu Tattauna