A cewar Lawal, zaman lafiya na dawowa a hankali a jihar ta Zamfara da ke yammacin arewacin Najeriya wacce ta jima tana fama da hare-haren barayin daji.
Marigayin ya rasu yana da shekaru 70, ya bar 'ya'ya fiye da 40. An kuma gudanar da jana'izarsa a ranar Alhamis, 6 ga Maris, 2025, inda dubban mutane daga ciki da wajen jihar suka halarta domin karramawa da yi masa addu'a.
Sanarwar na zuwa ne bayan da ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate ya bukaci dukkanin matakan gwamnati 3 su shigar da matasan cikin ma'aikatansu domin tallafawa aikin kokarin samar da kiwon lafiya ga kowa.
Manufar matakin ita ce karfafa hanyar samu da rage tsadar kayayyakin bukatu da ayyukan kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.
Hakan ya biyo bayan binciken da kwamitin majalisar a kan da'a da alfarma da bin dokokin zaman majalisa ya gudanar, wanda ya same ta da laifin saba dokokin majalisar dattawan.
Yayin da dalibai a wadannan jihohin arewa hudu ke ci gaba da hutu, takwarorinsu na sauran jihohin kasar na ci gaba da zuwa makaranta suna karatu, su kuwa 'yan Najeriya na ci gaba da tofa albarkacin bakinsu a kan batun inda suke kallonsa ta fuskoki mabambanta.
Abin da ya dauki hankali a wannan dambarwa shi ne a karon farko, shi da kansa Sanata Godswill Akpabio ya jagoranci zaman Majalisar a lokacin da Natasha ta gabatar da takardar korafin.
Hukumar zaben Ribas mai zaman kanta (RSIEC) ta tsayar da ranar 9 ga watan Agusta mai zuwa domin gudanar da sabon zaben kananan hukumomi a jihar.
Shugaban Majalisar Dattawan, wanda yace tun daga 25 ga watan Febrairun daya gabata yake shan kiraye-kirayen waya akan batun, kuma yana sane game da karuwar tattaunawa akan batun a kafafen sada zumunta.
An fara ambata Ogunjimi mai shekaru 57, a matsayin wanda zai maye gurbin madehin a watan Disamban da ya gabata.
An fara gudanar da bincike game da afkuwar lamarin sannan an gano tabarya da aka aikata laifin da ita domin gabatarwa a matsayin shaida.
Alkaluman baya bayan nan da TCN din ya fitar sun bayyana cewa matakin da kasar ta kai a bana shine mafi girma a cikin shekaru 4 da suka gabata.
Domin Kari
No media source currently available