A shekarar da ta gabata ne, kamfanin na NNPCL ya cimma yarjejeniyar cinikayya tsakaninsa da matatun cikin gida da kudin Naira, domin bunkasa tattalin arzikin kasar da kuma farfado da darajar kudin kasar.
Olufemi Soneye, dake matsayin shugaban sashin sadarwa na kamfanin NNPCL ya tabbatar da katsewar cinikayyar albarkatun man a kudin Naira tsakaninsu da sauran matatun mai dake cikin kasar, a wata sanarwa da kamfanin ya fitar dauke da sa hannun sa.
Olufemi, ya kara da cewa, “tun farko kamfanin na NNPCL ya cimma yarjejeniyar cinikayyar ne na tsawon watanni 6, wanda a karshen watan Maris din nan , yarjejeniyar cinikayyar ta zo karshe, kuma yanzu suna ci gaba da tattaunawa ta yadda za su sabunta yarjejeniyar”.
Eche Idoko, dake matsayin kakakin gamayyar kungiyoyin masu matatun mai na cikin gida ya tabbatar da katsewar cinikayyar a wani sako da ya aikewa manema labarai.
Idoko, ya ce “tabbas sun kawo karshen cinikayyar albarkatun mai tsakanin su da kamfanin na NNPCL, rubu’in farko a watan Maris da ake ciki, wanda kuma haka yake a cikin yarjejeniyar cinikayyar.
Idoko, ya kara da cewa, suna ci gaba da tuntubar bangaren gwamnatin kasar domin ta sabunta musu yarjejeniyar cinikayyar, wanda har izuwa yanzu ba’a cimma hakan ba.
A hirar shi da Muryar Amurka, Rilwan Ladan, daya daga cikin masu sharhi kan lamurran yau da kullum, na ganin gasar kayyade farashi tsakanin kamfanin albarkatun mai na NNPCL da kuma na Aliko Dangote, ya yi tasiri wajen rashin sabunta yarjejeniyar cinikayyar albarkatun mai a kudin Naira.
Rilwan, ya ce “kamfanin mai na Dangote, ya fara sauke farashin litar man fetur a kasar, wanda hakan ya farantawa ƴan kasar, sai dai kamfanin na NNPCL hakan bai yi musu dadi ba, idan aka yi la’akari da yadda suke kayyade farashi yadda suke so a baya”.
A nashi bayanin, Yusha’u Aliyu dake sharhi kan tattalin arziki a kasar, na ganin kamfanin mai na NNPCL yana daukar sauran kamfanonin matatun man fetur a matsayin kishiya, wanda kuma hakan ba zai haifarwa kasar da mai a ido ga tattalin arzikinta ba.
'Ƴan kasar dai na shaida ganin rangwamen farashin litar man fetur a kasar, bayan cimma yarjejeniyar cinikayyar tsakanin kamfanin NNPCL da kuma sauran kamfanonin matatun mai dake cikin kasar.
Saurari cikakken rahoto daga Rukaiya Basha:
Dandalin Mu Tattauna