Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Zartarwar Najeriya Ta Amince Da Kashe ₦10.3bn Kan Magungunan Kanjamau


Ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate
Ministan lafiya da walwalar al'umma, Ali Pate

Manufar matakin ita ce karfafa hanyar samu da rage tsadar kayayyakin bukatu da ayyukan kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.

A jiya Laraba, majalisar zartarwar tarayyar Najeriya ta amince da kashe kimanin naira biliyan 10.3 domin sayo magungunan rage karsashin cutar kanjamau, dana auna ciwon sukari da sauran muhimman bukatun kiwon lafiya.

Ministan lafiya da walwalar al'umma, Dr. Ali Pate, wanda ya yi jawabi ga manema labaran fadar gwamnati game da amincewar, yace manufar matakin ita ce karfafa hanyar samu da rage tsadar kayayyakin bukatu da ayyukan kiwon lafiya ga 'yan Najeriya.

'Yan makonnin da suka gabata, mun amince da samar kashin farko na magungunan rage karsashin kanjamau, kuma yanzu mun fitar da kudade kusan naira miliyan 997 domin ba da kwangilar sayo kashe na 3 na magungunan domin masu fama da cutar.

"Ina da yakinin cewar zaku fahimci muhimmancin yin hakan, duba da sauyin da aka samu game da daukar nauyin harkar lafiya a matakin kasa da kasa da kuma komawa kan daukar nauyi a cikin gida domin tabbatar da 'yan najeriya sun cigaba da samun kulawar da suke bukata," a cewarsa.

A cewar Pate, rukuni na 2 na kwangilolin sun hada da na sayo kayayyakin auna ciwon sukari da aka harhada a cikin Najeriya.

Ya kara da cewa an baiwa wani kamfani mai mazauni Legas kwangilar kera na'urorin gwajin ciwon sukarin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG